Wani rahoto da aka fitar, ya hakaito kwamandan rundunar sojin ruwan Amurka ta yankin tekun Indiya da Pacific na cewa, tun bayan ganawar shugabannin Sin da Amurka a watan da ya gabata, Sin ta rage ayyukan soji na dakile jiragen saman yakin Amurka.
Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana yayin taron manema labarai na Talatar nan cewa, har kullum, kasar Sin na adawa da yadda Amurka ke yawan tura jiragen ruwan ta, da jiragen saman yaki dake kutse a kewayen sassan ruwa da na samaniyar Sin, kuma Sin din na fatan Amurka za ta gyara wadannan matakai masu hadarin gaske, wadanda ka iya yin barazana ga tsaron kasar Sin, da hadarin jefa yankin cikin tashin hankali.
A wani batun mai nasaba kuma, yayin da yake tsokaci game da kalaman jakadan Amurka a Sin mista Robert Nicholas Burns don gane da batun Gabas ta Tsakiya, Wang Wenbin ya ce kasar Sin ba ta da wani son rai game da batun Gabas ta Tsakiya, kuma ba ta amince da kirkirar wani gungun goyon bayan wani bangare ba. Wang ya ce har kullum Sin na goyon bayan matakin kasashen Gabas ta Tsakiya, da al’ummun yankin, na jibintar lamurran yankin su yadda suke so. (Mai fassara: Saminu Alhassan)