A shekarun baya bayan nan kasar Sin na kara matsa kaimin ganin ta sauke nauyin dake wuyanta, na babbar kasa mai samar da kyakkyawan tasiri a duniya. Kuma a gabar da duniya ke fuskantar manyan kalubalen tsaro, Sin na ci gaba da kara azamar bayar da gudunmawa ga matakan shawo kan wannan kalubale.
Hakan ne ma ya sa ko da a baya bayan nan, yayin ganawar shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Masar a birnin Alkahira, shugaba Xi ya jaddada matsayar Sin ta ci gaba da taimakawa kasashen yankin gabas ta tsakiya, wajen kyautata alakar kawance da makwabtaka, da lalubo hanyar gina sabon tsarin tsaro a yankin, da nufin samar da cikakken hadin kai da ingantaccen tsaro mai dorewa.
Domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na dogon lokaci a yanking gabas ta tsakiya, shugaba Xi ya gabatar da wasu shawarwari masu muhimmancin gaske guda hudu, ciki har da wajibcin kara himma wajen karfafa harkokin tsaron cikin gida domin samar da tsaron bai daya na yankin, sannan a samar da cikakkiyar hanyar bunkasa tsaron bai daya, da karfafa tubalin tsaron bai daya ta hanyar bunkasa ayyukan ci gaba, sannan a samar da hadin kan kasa da kasa domin karfafa tsaron bai daya na yankin.Alal hakika, wannan shawara ta Sin ta nuna yadda kasar ta himmatu wajen bayar da gudunmawarta a zahiri, domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Tabbas, gina sabon tsarin tsaro a yankin gabas ta tsakiya na bukatar karfafa harkokin tsaron cikin gida. Kazalika, ya zama wajibi al’ummun yankin gabas ta tsakiya su zama masu jagorantar al’amuransu, sa’anan kasashen yankin su karbi ragamar jagorancin harkoki da tsaron kansu.
A daya hannun kamata ya yi sauran sassan kasa da kasa, musamman kasashe masu fada a ji su kwaikwayi himmar kasar Sin a fannin tallafawa matakan dawo da zaman lafiya mai dorewa a yankin. (Saminu Alhassan)














