Dakarun Sojojin Nijeriya na Shiyya 6, karkashin shirin ‘Operation Enduring Peace (OPEP)’, sun ceto fasinjoji uku da suka samu raunukan harbin bindiga a lokacin da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai hari kan hanyar Jos–Makarfi a ƙaramar hukumar Riyom ta Jihar Filato.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 1 na dare ranar Alhamis, 10 ga Satumba, 2026, bayan dakarun sun samu rahoton cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun tare hanyar tare da fara harbe-harbe ba-zata.
Bayan isa wurin, sojojin sun tarar da wata motar haya mai lambar EPE-840XB, wadda wani direba mai suna Baba Ruwa daga Jihar Oyo ke tukawa, bayan da maharan suka tare ta.
Rahoton ya ce waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutanen sun tsere da hangen sojojin, lamarin da ya ba dakarun damar ceto fasinjoji uku da suka samu raunukan harbin bindiga.
An kuma kwashe waɗanda suka jikkata domin ba su kulawa a asibiti.













