A yau Alhamis, an gudanar da taron manema labarai game da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar tsaron jama’a na duniya na shekarar 2026 a birnin Lianyungang, dake lardin Jiangsu na kasar Sin.
Yayin taron na wannan karo, an fitar da “rahoton alkaluman yanayin tsaron jama’a na duniya tsakanin shekarar 2025 zuwa shekarar 2026”. Alkaluman na wannan shekara sun shafi kasashe 62, wadanda ke kunshe da kaso 82.73 bisa dari na al’ummar duniya, da kaso 75.22 bisa dari na fadin kasar duniyarmu, da kuma kaso 87.47 bisa dari na jimillar tattalin arzikin duniya.
Rahoton ya nuna cewa, kasashe 10, ciki har da kasashen Sin, da Singapore, da Uzbekistan da dai sauransu, sun samu maki 80 ko fiye da haka. Kuma, kasar Sin ce ta zo ta farko da maki 84.62 a fannin tabbatar da tsaron jama’a. (Mai Fassara: Maryam Yang)














