Hukumar wasanni ta kasa (NSC) ta tabbatar da biyan kudin da yakai Dalar Amurka 100,000 ga kowace yar wasar tawagar kwallon kwando ta mata ta Nijeriya wadda akafi sani da D’Tigress, a matsayin wani bangare na karramawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu yayi masu saboda nasarar da suka samu na lashe gasar FIBA Women’s Afrobasket ta shekarar 2025.
Hukumar ta kuma tabbatar da biyan kudin da yakai dalar Amurka 50,000 ga kowane jami’in tawagar kwallon Kwandon ta mata, Hukumar ta NSC ta tabbatar da cewar an kammala saka kudaden a asusun ajiyar yan wasan yayinda duka wadanda suka cancanci samun kudin suka tabbatar da samun kudin a ranar 9 ga watan Satumbar wannan shekarar ta 2026, tawagar D’Tigress ta lashe gasar FIBA Women’s Afrobasket a karo na biyar a jere, wanda hakan yasa ta kafa tarihin zama kasar da tafi yawan lashe gasar, inda ta lashe sau Bakwai a tarihi.
Hukumar ta ce wannan biyan kudin wani bangare ne na irin kyaututtukan da Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin bai wa tawagar, a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na hukumar, Kehinde Ajayi, ya sanya wa hannu a ranar Laraba, NSC ta bayyana cewa kyaututtukan da Shugaban Kasar yayi alkawarin bayarwa sun hada da gidaje masu dakuna uku a Abuja, lambobin yabo na kasa (Order of the Niger), da kuma kudaden.Hukumar ta kuma bayyana cewar tun kafin yanzu yan wasa da jami’an tawagar sun karbi takardun mallakar gidajensu masu dakuna uku a Abuja da kuma takardun shaidar lambobin yabo na kasa a watan Fabrairun 2026, yayin wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIBA a birnin Lyon na kasar Faransa.
Hukumar ta kuma bayyana cewa tawagar kwallon kafa ta mata ta Nijeriya (Super Falcons), wadda ita ma aka yi wa alkawarin kyaututtukan, ta riga ta karbi takardun mallakar gidajensu masu dakuna uku a Abuja da kuma takardun shaidar lambobin yabo na kasa, abinda kawai ya rage yanzu shi ne kudade wadanda zasu shiga hannunsu nan bada jimawa ba.














