ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Dauki Matakin Mayar Da Martani Kan Sayar Da Makaman Amurka Ga Yankin Taiwan Na Kasarta

by Sulaiman
7 months ago

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Shafin intanet na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya fitar da wani sako a yau Jumma’a 26 ga wata, inda ya bayyana cewa, a matsayin martani ga sabuwar sanarwar da Amurka ta fitar ta sayar da manyan makamai ga yankin Taiwan na kasar Sin, kasar ta Sin ta yanke shawarar daukar matakan da suka dace bisa dokar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin game da tinkarar takunkumin kasashen waje, a kan kamfanoni 20 na Amurka da ke da alaka da sojan Amurka da kuma wasu shugabanni 10 na kamfanoni, wadanda suke da hannu dumu-dumu wajen samar da makamai ga Taiwan a ‘yan shekarun nan.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya jaddada cewa, batun Taiwan yana sahun gaba a cikin manyan muradun kasar Sin, kuma kan iyaka ne da ya zama wajibi kada a tsallaka a huldar Sin da Amurka. Duk wanda ya yi yunkurin ketare iyakar da yin tsokana game da batun Taiwan, zai gamu da martanin kasar Sin. Sannan, duk wani kamfani ko mutumin da ke sayar da makamai ga Taiwan zai girbi abin da ya shuka. Babu wata kasa ko wani karfi da zai taba raina kuduri, da karfin ikon da gwamnati da jama’ar kasar Sin ke da su na kiyaye ‘yancin kai da kare martabar yankin kasar.

Mai magana da yawun ma’aikatar ya kuma bayyana cewa, kasar Sin ta sake yin kira ga Amurka da ta mutunta ka’idar Sin daya tilo a duniya da kuma sanarwar hadin gwiwa guda uku wadda Sin da Amurka suka fitar, da cika alwashin da shugaban Amurka ya dauka, da dakatar da yunkuri mai hatsari na bai wa Taiwan makamai, da dakatar da kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan, da kuma dakatar da yi wa ‘yan awaren Taiwan ingiza mai kantu ruwa a kan “’yancin kan Taiwan”. Kasar Sin za ta ci gaba da daukar kwararan matakai don tabbatar da cikakken ikon kasarta, tsaro da kuma cikakken kare martabar yankinta. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

ADVERTISEMENT
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya
  • Sulaiman
    Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026
  • Sulaiman
    An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”
  • Sulaiman
    Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

MASU ALAKA

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya
Daga Birnin Sin

July 14, 2026

Next Post
Tinubu Bai Taɓa Ba Ni Umarnin Yin Ƙarya Ko Cin Zarafin ’Yan Jarida Ba – Minista

Tattalin Arzikin Nijeriya Ya Bunkasa A 2025 — Minista

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci