Ma’aikatar tsaron cikin gida ta Amurka ta sanar da saka wasu kamfanonin kasar Sin guda uku, cikin jerin sunayen kamfanonin da Amurkan ta kakaba wa takunkumi bisa wai “Dokar hana aikin tilas a yankin Uyghur”, a jiya Labara.
Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, ya ce babu inda ake tilasawa mutane yin aikin tilas a Sin, kuma al’ummun kabilu daban-daban na jihar Xinjiang suna da ’yancin yin aiki bisa daidaito, kuma ana kare hakkokin aikinsu yadda ya kamata bisa doka.
Ya ce matakan da Amurka ta dauka ba su da tushe na gaskiya ko kadan, kana Amurka na ci gaba da fakewa da batun “hakkokin dan adam” don ba da kariya ga ra’ayin bangaranci da babakere. Don haka kasar Sin ta yi Allah wadai da hakan da kakkausar murya, kuma tana adawa sosai da matakin.
Ba da dadewa ba Amurka ta saka wasu kamfanoni da dama na Sin cikin jerin sunayen kamfanonin da ta kakaba wa takunkumi bisa dokar da ake kira dokar da ta shafi yankin Xinjiang, kuma nan da nan Sin ta bayyana rashin jin dadi, tare da mayar da martani, inda ta bukaci Amurka da ta dakatar da siyasantarwa, da shafawa wasu sassa bakin fenti, kuma ta daina yin matsin lamba marar dalili kan kamfanonin Sin. (Amina Xu)













