ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 30, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Kama Mutane 4 Masu Taimaka Wa Ƴan Bindiga A Binuwai

by Abubakar Sulaiman
2 hours ago

Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa na Sojin Nijeriya, Operation Whirl Stroke, sun kama mutum biyu da ake zargi da safarar kayayyakin amfani ga ƴan bindiga, da wasu mutum biyu da ake zargi da fashi da makami a jihar Binuwai.

An gudanar da kamen ne a ranar Laraba, 28 ga Oktoba, 2026, a ƙananan hukumomin Katsina-Ala da Ukum, bayan samun bayanan sirri da kuma rahoton fashi da makami.

Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na shalƙwatar rundunar, Laftanar Ahmad Zubairu Zubairu, ya ce dakarun sashi na ɗaya sun kama waɗanda ake zargin masu samar da kayayyakin masarufi ne ga ƴan bindiga a yankin Abaji. An bayyana sunayensu da Tertser Terngu, mai shekara 24, da Aondongu Tersoo, mai shekara 15, waɗanda dukkansu suka fito daga ƙauyen Tersoo.

ADVERTISEMENT

A cewar sanarwar rundunar, ana zargin mutanen biyu da taimaka wa wani jagoran ƴan bindiga da ke gudanar da ayyukansa a yankin Kogin Yooyo, cikin Ƙaramar Hukumar Katsina-Ala. Rundunar ta ce an tsare su domin gudanar da bincike da kuma ɗaukar matakan da suka dace bisa doka.

A wani sumamen na daban, dakarun da ke sintiri sun samu rahoton wani fashi da makami da ya faru da misalin ƙarfe 2:16 na rana a ƙauyen Jootar, kan hanyar Kyado zuwa Wukari, cikin Ƙaramar Hukumar Ukum. Lokacin da sojojin suka isa wurin, sun tarar da jami’ai masu gadin sa-kai sun riga sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a fashin. An kwato bindiga ƙirar gida, da harsasai bakwai nau’in 7.62mm PKT da almakashi guda.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Umarci EFCC Ta Sa Ido Kan Kuɗaɗen Da Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ke Samu

Sabon Bashin Da Zamu Ciyo Zai Buɗe Damarmaki Ga Nijeriya – Tinubu

Kwamandan Operation Whirl Stroke kuma Babban Kwamandan Runduna ta Biyar ta Sojin Ƙasa, Manjo-Janar Moses Gara, ya yaba wa dakarun bisa ƙoƙarinsu.

Ya buƙace su da su ci gaba da yin taka-tsantsan, da amfani da sahihan bayanan sirri da kuma ƙarfafa sintiri domin yaƙi da ayyukan ƴan bindiga da sauran laifuffuka a yankin.

Rundunar ta ce waɗannan sumame na cikin ƙoƙarin da take yi na inganta tsaro a jihar Binuwai.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Tinubu Ya Umarci EFCC Ta Sa Ido Kan Kuɗaɗen Da Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ke Samu
  • Abubakar Sulaiman
    Sabon Bashin Da Zamu Ciyo Zai Buɗe Damarmaki Ga Nijeriya – Tinubu
  • Abubakar Sulaiman
    Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano
  • Abubakar Sulaiman
    NLC Ta Buƙaci Ƴan Jarida Su Tursasa Ƴan Siyasa Kan Mafi Karancin Albashi

MASU ALAKA

Tinubu Ya Umarci EFCC Ta Sa Ido Kan Kuɗaɗen Da Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ke Samu
Labarai

October 29, 2026
Sabon Bashin Da Zamu Ciyo Zai Buɗe Damarmaki Ga Nijeriya – Tinubu
Labarai

Sabon Bashin Da Zamu Ciyo Zai Buɗe Damarmaki Ga Nijeriya – Tinubu

October 29, 2026
Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano
Manyan Labarai

Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano

October 29, 2026
Next Post
Sin Ta Mayar Da Martani Ga Amurka Game Da Kakaba Wa Kamfanoninta Takunkumi Dangane Da Batun Xinjiang

Sin Ta Mayar Da Martani Ga Amurka Game Da Kakaba Wa Kamfanoninta Takunkumi Dangane Da Batun Xinjiang

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Mayar Da Martani Ga Amurka Game Da Kakaba Wa Kamfanoninta Takunkumi Dangane Da Batun Xinjiang

Sin Ta Mayar Da Martani Ga Amurka Game Da Kakaba Wa Kamfanoninta Takunkumi Dangane Da Batun Xinjiang

October 29, 2026
Sojoji Sun Kama Mutane 4 Masu Taimaka Wa Ƴan Bindiga A Binuwai

Sojoji Sun Kama Mutane 4 Masu Taimaka Wa Ƴan Bindiga A Binuwai

October 29, 2026
An Kammala Cikakken Zama Na JKS Inda Aka Amince Da Kudurin Ci Gaba Da Bin Cikakken Tsarin Shugabancin Kai Na Jam’iyyar

Xi Ya Mika Sakon Ta’aziyya Game Da Karon Da Jiragen Kasa Suka Yi A Spain Da Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane

Xi Ya Mika Sakon Ta’aziyya Game Da Karon Da Jiragen Kasa Suka Yi A Spain Da Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane

October 29, 2026
Sabon Bashin Da Zamu Ciyo Zai Buɗe Damarmaki Ga Nijeriya – Tinubu

Sabon Bashin Da Zamu Ciyo Zai Buɗe Damarmaki Ga Nijeriya – Tinubu

October 29, 2026
Tinubu Ya Umarci EFCC Ta Sa Ido Kan Kuɗaɗen Da Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ke Samu

Tinubu Ya Umarci EFCC Ta Sa Ido Kan Kuɗaɗen Da Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ke Samu

October 29, 2026
Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano

Tsaro: Rundunar Sojoji Ta Aike Da Sabuwar Bataliya Zuwa Kano

October 29, 2026
Yi Wa Kanta Kwaskwarima, Wata Hanya Ce Da JKS Ke Amfani Da Ita Wajen Daidaita Matsalolin Mulkin Kasa

Yi Wa Kanta Kwaskwarima, Wata Hanya Ce Da JKS Ke Amfani Da Ita Wajen Daidaita Matsalolin Mulkin Kasa

October 29, 2026
NLC Ta Buƙaci Ƴan Jarida Su Tursasa Ƴan Siyasa Kan Mafi Karancin Albashi

NLC Ta Buƙaci Ƴan Jarida Su Tursasa Ƴan Siyasa Kan Mafi Karancin Albashi

October 29, 2026
Sin Ta Fadada Kasuwanci Ga ‘Yan Kasashen Waje A Kasuwar Cinikayya Cikin ‘Yanci Mafi Girma A Duniya

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci