Hukumar kula da yanayi ta kasar Sin (CMA) ta mika sabuwar manhajar MAZU, mai aikewa da gargadin gaggawa wadda kasar Sin ta kera da ke amfani da fasahar kirkirarriyar basira ta AI, ga kasar Djibouti a yau Jumma’a a hukumance, a wani karamin taro na bangaren taron duniya kan fasahar AI na shekarar 2026 da kuma babban taron manyan jami’ai kan tafiyar da sha’anin fasahar AI a duniya a birnin Shanghai na kasar Sin.
A watan Yulin 2025 ne dai, kasar Sin ta bai wa Djibouti kyautar MAZU-Urban, wata manhajar fasaha mai aikewa da gargadin gaggawa da ke amfani da fasahar AI, domin rigakafin aukuwar bala’o’i daban-daban.
Wannan sabuwar manhaja tana kara ingancin hasashen yanayi ta hanyar rage tazarar da ake aunawa daga kilomita 9 zuwa kilomita 3, tare da bayar da hasashen yanayi na gabanin lokaci na tsawon kwanaki uku da kuma sabunta bayanan a duk bayan sa’o’i shida. (Mai fassara: Abdulraazaq Yahuza Jere)














