Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya gudanar da taron manema labarai da misalin karfe 10 na safe a yau, inda ya gabatar da yanayin bayanin mu’amalar kudade tsakanin mazauna Sin da ’yan kasashen waje a rabin farko na shekarar 2026.
Bayanan hukumar kula da kudaden waje ta kasar sun nuna cewa, a rabin farkon shekara, jimillar mu’amalar kudaden ta hanyar bankuna ta kai dala tiriliyan 9.2, wadda ta karu da kashi 21% idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar da ta gabata.
Ban da wannan kuma, jimillar musayar kudaden waje a bankuna ta kai dala tiriliyan 2.9, wadda ta karu da kashi 24% bisa na makamancin lokacin bara, duk wadannan alkaluma sun karu zuwa wani sabon matsayi a tarihi a tsakanin wannan lokaci.
Kazalika, cinikin waje na kasar Sin ya ci gaba da tafiya yadda ya kamata, kuma harkar zuba jari na kara habaka. (Amina Xu)














