ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA

by Sulaiman and CGTN Hausa
2 months ago
Xi

A yau Jumma’a 17 ga watan Yuli, shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya gana da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD), António Guterres, a birnin Shanghai. Guterres ya ziyarci kasar Sin ne domin halartar taron duniya kan fasahar AI na shekarar 2026 da kuma taron manyan jami’ai game da tafiyar da sha’anin AI a duniya.

Xi Jinping ya bayyana cewa, kamar yadda ta saba, kasar Sin za ta kara karfafa hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya domin karfafa manufar zaman lafiya da ci gaban duniya, tare da inganta gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga bil’adama.

A nasa bangare, Guterres ya bayyana cewa, kasar Sin ta ci gaba da yin tsayin daka wajen nuna cikakken goyon baya ga tsarin hadin kan mabambantan bangarori, da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya, da kuma hadin gwiwar kasa da kasa, inda ta zama abar koyi ga sauran kasashen duniya. Majalisar Dinkin Duniya za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da kasar Sin domin kare muradun al’ummar duniya na bai-daya.

ADVERTISEMENT

Kana ya gana da firaministan Thailand, Anutin Charnvirakul a birnin Shanghai. Anutin ya ziyarci kasar Sin ne domin halartar taron duniya kan fasahar kirkirarriyar basira ta AI na shekarar 2026 da kuma babban taron manyan jami’ai game da tafiyar da sha’anin fasahar AI a duniya, kana da gudanar da ziyarar aiki a kasar.

Xi Jinping ya bayyana cewa, ya kamata kasar Sin da Thailand su hanzarta gina layin dogo da zai sada kasashen biyu da kuma hade layin dogo na tsakanin Sin, da Laos, da kuma Thailand, tare da fadada hadin gwiwa a sabbin fannoni kamar fasahar AI, da harkar sararin samaniya, da makamashi mai tsafta.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

A nasa bangaren, Anutin ya bayyana cewa, kasar Thailand a shirye take ta karfafa hadin gwiwa da kasar Sin domin karfafa zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da ci gaba, da samun wadata a yanki da ma duniya baki daya.

Kazalika, duk da a yau din, Xi Jinping ya gana da firaministan Cambodia, Hun Manet, wanda shi ma ya zo kasar Sin ne domin halartar taron duniya kan fasahar kirkirarriyar basira ta AI na shekarar 2026. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Xi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang
  • Sulaiman
    Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris
  • Sulaiman
    Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu
  • Sulaiman
    Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya
Xi
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

MASU ALAKA

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
Daga Birnin Sin

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Next Post
Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura

Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura

LABARAI MASU NASABA

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026
Xi

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Xi

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026
Xi

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.