ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Huning Ya Ziyarci Koriya Ta Arewa

by CGTN Hausa and Sulaiman
25 seconds ago
Wang

Bisa gayyatar kwamitin tsakiyar jam’iyyar ‘yan kwadago ta Koriya ta Arewa da gwamnatin Koriya ta Arewa, memban kwamitin dindindin na ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Sin JKS, kuma shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siaysa ta kasar Wang Huning, ya jagoranci tawagar wakilai domin ziyarar aiki a Koriya ta Arewa daga ranar 15 zuwa 17 ga watan Yuli.

A birnin Pyongyang, ya gana da babban sakataren jam’iyyar ‘yan kwadago ta Koriya ta Arewa, kuma shugaban kasar Kim Jong-un.Wang Huning ya isar da sahihiyar gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga Kim Jong-un yayin ganawar tasu.

Wang Huning ya bayyana cewa, bana ita ce ta cika shekaru 65 da sanya hannu kan “Yarjejeniyar abota da hadin gwiwa tsakanin Sin da Koriya ta Arewa”. Ziyarar da shugaba Xi ya kai Koriya ta Arewa kwanan nan, ta samu cikakkiyar nasara. Shugabannin biyu sun gudanar da tattaunawa mai zurfi, kuma sun cimma jerin muhimman yarjejeniyoyi, wadanda suka kafa kyakkyawar makoma ga ci gaban dangantakar Sin da Koriya ta Arewa a sabon zamani, da kuma kara wa ayyukan gurguzu na kasashen biyu kuzari.

ADVERTISEMENT

A nasa bangare, Kim Jong-un ya mika gaisuwarsa ga shugaba Xi, ya kuma taya jam’iyyar kwaminis ta Sin murnar cika shekaru 105 da kafuwa.

Kim Jong-un ya kara da cewa, bangaren Koriya ta Arewa zai ci gaba da dora babban muhimmanci kan raya dangantakar Koriya ta Arewa da Sin, kuma zai kara tunbubar manyan shugabanni da bangaren Sin, da zurfafa musayar ra’ayi kan dabarun gudanar da harkokin jam’iyya, da karfafa amincewar siyasa tsakaninsu, da kuma fadada hadin gwiwa a fannoni kamar tattalin arziki, da fasaha, da kiwon lafiya, da al’adu da sauransu, domin amfanar da al’ummomin kasashen biyu.(Amina Xu)

LABARAI MASU NASABA

Yawan Mu’amalar Kudi Tsakanin Mazauna Sin Da ’Yan Kasashen Waje Ya Hau Wani Sabon Matsayi A Tarihi

Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Wang
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

    Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

    Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030
Wang
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman

MASU ALAKA

Yawan Mu’amalar Kudi Tsakanin Mazauna Sin Da ’Yan Kasashen Waje Ya Hau Wani Sabon Matsayi A Tarihi
Daga Birnin Sin

July 17, 2026

July 16, 2026

LABARAI MASU NASABA

Wang Huning Ya Ziyarci Koriya Ta Arewa

Wang Huning Ya Ziyarci Koriya Ta Arewa

July 17, 2026
Yawan Mu’amalar Kudi Tsakanin Mazauna Sin Da ’Yan Kasashen Waje Ya Hau Wani Sabon Matsayi A Tarihi

Yawan Mu’amalar Kudi Tsakanin Mazauna Sin Da ’Yan Kasashen Waje Ya Hau Wani Sabon Matsayi A Tarihi

July 17, 2026
Gasar Kofin Duniya: Da Ƙarfinmu Muka Kawo Matakin Da Muke Yanzu – Messi

Matatar Man Dangote Ta Dawo Sayar Da Fetur A Dala

Matatar Man Dangote Ta Dawo Sayar Da Fetur A Dala

July 17, 2026
Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi

July 17, 2026
Falalar Salatut Tasbihi

Falalar Salatut Tasbihi

July 17, 2026
A Baya Ba A San Jihar Kano Da Harkar Daba Ba – Tsohon Shugaban NAHCON

Direba Ya Hallaka Ɗalibar Jami’ar Kiwon Lafiya Ta Azare, Ya Gudu

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci