ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura

by Yusuf Shuaibu
2 months ago
Muslim

Matakin Shugaba kasa Bola Tinubu na ci gaba da tafiya da mataimakin shugaba kasa, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a zabe 2027 ta sake kunno sabon muhawara kan tikitin Musulmi-Musulmi na jam’iyyar APC.

Tabbatar da Shettima a zaben 2027 ya bude sabuwar muhawara game da tikitin APC na Musulmi-Musulmi, inda jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki kawunansu ya rabu kan ko addini ko kwarewa ne ya kamata ya yi tasiri a sha’anin shugabanci.

Matakin jam’iyyar APC ya kawo karshen hasashen cewa Tinubu zai iya maye gurbin Shettima da Kirista daga Arewa, yayin da ta sake tayar da muhawara kwatancin ta zaben 2023.

ADVERTISEMENT

Ko da yake masu sukar sun yi jayayya cewa tikitin addini daya na iya rage daidaiton addini a Nijeriya, Tinubu da Shettima sun lashe zaben shugaban kasa, kuma jam’iyyar da ke mulki yanzu ta zabi ta ci gaba da wannan hadin don yin wa’adi na biyu.

Yayin da wasu jam’iyyun adawa, ciki har da APGA da YPP, suka soki tikitin muslim-muslim, wasu sun gargadi cewa daidaiton addini har yanzu yana da muhimmin a siyasar Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Sabon muhawara ta biyo bayan tabbacin da APC ta bayar a ranar Juma’a cewa Tinubu zai yi takara a zaben 2027 tare da Shettima, matakin da ya kawo karshen abun da ake tsammani cewa shugaba kasa zai zabi Kiristocin Arewa a matsayin mataimakin takararsa.

Kafin sanarwar, an danganta wasu sunaye da wannan mukamin, ciki har da ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya) da Bishof Hassan Kukah da tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

Matakin APC ta tayar da muhawara da ta mamaye zaben 2023, a lokacin da ake ganin cewa Tinubu, Musulmi ne daga Kudu Maso Yamma, ya zabi Shettima, wanda shi ma Musulmi ne daga Arewa Maso Gabas, a matsayin abokin takararsa.

Masu suka sun yi ikirarin cewa tikitin ya karya al’adar siyasar Nijeriya ta daidaita tikitin shugaban kasa a tsakanin addinai. Duk da haka, Tinubu da Shettima sun ci zabe, sun doke ‘yan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da jam’iyyar LP, Peter Obi da jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso.

Da take mayar da martani kan lamarin, APGA ta ce ya kamata a mayar da hankali wajen zaben shugabanci na cancanta maimakon addini.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Ejimofor Opara, ya ce Nijeriya ta wuce yin siyasar bambancin kuma a yi wa shugabanni hukunci bisa ga aikinsu.

“Ya kamata kwarewa ta kasance batun da ke tantance komai a 2027, ba ko ‘yan takara Musulmai ne ko Kiristoci ba,” in ji shi.

Jam’iyyar YPP ta kuma yi ikirarin cewa hali, kwarewa da gaskiya su fi muhimmanci fiye da la’akari da addini ko kabila wajen zaben shugabanci.

Mai magana da yawun jam’iyyar, Wale Egbeola-Martins, ya ce babban kalubalen Nijeriya shi ne, rashin kyakkyawan jagoranci fiye da addinan wadanda ke mulki.

“Asalin kalubalen da kasarmu ke fuskanta tun dawowar mulkin dimokuradiyya ba kabila ko addinin wadanda ke mulki ba ne, amma rashin kyakkyawan jagoranci ke damun kasarmu,” in ji shi.

Jam’iyyar ta ce za ta ci gaba da goyon bayan siyasa bisa cancanta da muradin kasar maimakon la’akari da addini ko kabila.

A halin yanzu, APC ta kare matakinta na sake daukar Shettima, tana jaddada cewa zabin ya dogara ne kan muradin kasa da kuma nazarin halin siyasar kasar nan.

Daraktan yada labarai na jam’iyya, Bala Ibrahim, ya ce tikitin Muslim-Muslim bai haifar da tashin hankali na addini da masu sukar suka hasashen ba kafin zaben 2023.

“An cimma wannan matakin ne bayan an yi cikakken nazari kan halin da ake ciki. Jam’iyyar tana sane da tasirin addini amma kuma tana la’akari da muradun Nijeriya gaba daya,” in ji shi.

Ibrahim ya yi watsi da tsoron cewa tikitin na iya haifar da rabuwar addini, yana ikirarin cewa gwamnati ta inganta zaman lafiya tsakanin addinai tun lokacin da ta karbi mulki.

Shugaban jam’iyyar ADP, Yabagi Yusuf, da kuma wani jagoran hadin kan jam’iyyun siyasa, Mark Adebayo, sun kawo hujja cewa batutuwan da suka shafi tsaro, tattalin arziki da kuma yadda gwamnati ke aiki ne za su fi rinjaya a yakin neman zaben 2027 fiye da bambancin addini.

Yusuf ya ce matakin jam’iyyar APC ta samu tasiri sosai ne daga abubuwan da suka shafi zabe, musamman bukatar samun goyon baya a manyan wurare da ke da masu jefa kuri’a da yawa.

Ya yi ikirarin cewa yayin da la’akari da addini ke ci gaba da kasancewa wani bangare na tattaunawar siyasa, jam’iyyu a karshe suna la’akari da karfin zabe da yarda da ‘yan takararsu lokacin yanke hukunci.

Yusuf ya ce matakin APC ta samo asali ne daga lissafin zabe ba daga la’akari da addini ba.

A cewarsa, jam’iyyun siyasa suna mai da hankali ne wajen hada jerin ‘yan takara da za su iya samun goyon bayan masu kada kuri’a da yawa.

Tsohon sakataren yada labarai na hadakar jam’iyyun Siyasa, Mark Adebayo, ya bayyana cewa tikitin Muslim-Muslum ba zai haifar da cece-kuce kamar yadda ya yi a shekarar 2023 ba.

Ya ce batutuwa kamar tsaro, tattalin arziki da shugabanci za su mamaye yakin neman zaben 2027.

Haka nan kungiyar matasa ta Ijaw (IYC) ta yi watsi da shaidar addini a matsayin tushe na tantance shugabannin siyasa.

Shugaban IYC, Jonathan Lokpobiri, ya ce ‘yan Nijeriya su mai da hankali kan cancanta da kyakkyawan shugabanci maimakon addinin ‘yan takara.

“Abin da muke bukata shi ne, kyakkyawan shugabanci wanda zai iya yanke hukunci masu wahala kuma ya inganta rayuwar ‘yan Nijeriya. Addini bai kamata ya zama ma’aunin shugabanci ba,” in ji shi.

Sai dai kuma, gamayyar kungiyar shugabannin matasa na Kudu maso Gabas sun suki matakin APC, sun bayyana tikitin Muslim-Muslum a matsayin lamari na nuna bambancin addini a Nijeriya.

Shugaban gamayyar, Goodluck Ibem, ya ce watsi da nada Kirista daga Arewacin Nijeriya na iya kara jin an ware su a tsakanin ’yan Nijeriya.

Haka kuma, kungiyar matasa ta Kudu maso Kudu ta yi watsi da sake zabar Shettima.

Shugaban kungiyar, Imeabe Oscar, ya bayyana cewa matakin APC ta kasance ta siyasa kuma ya zargi jam’iyyar da sake maimata zabar mataimakin shugaban kasa, musamman don samun fa’ida wajen zabe a Arewan Nijeriya.

Muslim
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Sin Ta Yaba Da Matakin Amurka Na Kin Tsawaita Dokar Ta-Baci Dangane Da HK

Sin Ta Yaba Da Matakin Amurka Na Kin Tsawaita Dokar Ta-Baci Dangane Da HK

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.