Hukumar lura da abinci da tsumin hatsi ta kasar Sin, ta ce kasar za ta raba nasarorin da ta cimma, bisa dabarun bai daya na bunkasa samar da tabbacin abinci tsakanin yankin Asiya da tekun Fasifik da al’ummunsu, bisa adalci da game kowa da kowa.
Da yake tabbatar da hakan a ranar Alhamis, yayin wani taron manyan jami’ai na gwamnatoci, da sassa masu zaman kansu na kungiyar APEC, dangane da lalubo hanyoyin samar da tabbacin abinci, shugaban hukumar Liu Huanxin, ya gabatar da wasu shawarwari masu nasaba, yana mai jaddada muhimmancin karfafar juna a fannin dijital.
A cewarsa, kasar Sin za ta goyi bayan fadada amfani da dabaru, wajen samar da tabbaci a tsarin samar da isasshen hatsi, da fadada amfani da fasahar AI, da fasahohin kimiyya, da amfani da na’urori masu basira wajen gudanar da ayyuka a wannan fanni.
Liu Huanxin, ya kuma yi kira da a yaukaka hadin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnatoci, da sassan kasuwanci, da cibiyoyin bincike da hukumomin kasa da kasa, ta yadda za a kara budewa, da cimma gajiyar bai daya a fannin hadin gwiwar samar da tabbacin isasshen hatsi.
An gudanar da taron ne a birnin Dalian, na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin, ya kuma hallara kusan wakilai 150 daga sassan gwamnatoci, da kungiyoyin ‘yan kasuwa, da cibiyoyin bincike, da hukumomin membobin kungiyar APEC. (Saminu Alhassan)













