ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, October 28, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Majalisar Dokokin Sakkwato Ta Amince Da Kafa ’Yansandan Jihohi

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
2 hours ago

Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta amince da ƙudirin gyaran Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 domin bai wa jihohi damar kafa rundunonin ’yansanda na kansu.

LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewa majalisar ta amince da ƙudirin ne bayan Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Mustapha Abdullahi, ya gabatar da shi a zaman majalisar na ranar Laraba.

Da yake gabatar da ƙudirin, Abdullahi ya ce an tsara gyaran ne domin bai wa jihohi damar kafa rundunonin ’yansanda na kansu.

ADVERTISEMENT

Ya bayyana cewa ɓangaren zartarwa ne ya aika da ƙudirin, wanda Majalisar Dattawa ta duba a ranar 24 ga watan Yuni, yayin da Majalisar Wakilai ta yi nazari a kansa a ranar 23 ga watan Yuli.

Daga bisani, an miƙa shi ga Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato a ranar 22 ga watan Satumba.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Shirin Bayar Da Lamunin Gidaje Mara Kuɗin Ruwa A Kano

Kaduna Za Ta Mayar Da Yaran Da Ba Su Zuwa Makaranta 187,000 Makaranta Cikin Shekara 1

A cewarsa, tsarin da ƙudirin ya tanada zai fayyace ayyukan rundunar ’yansandan tarayya da na jihohi domin inganta tsaro da magance matsalolin tsaro a sassan ƙasar nan.

Ya ce rundunar ’yansandan tarayya za ta mayar da hankali kan manyan laifukan da suka shafi jihohi, ta’addanci, laifuka a yanar gizo, tsaron iyakokin ƙasa, tsaron Babban Birnin Tarayya, da kuma kare kadarorin gwamnatin tarayya.

A ɗaya ɓangaren, ya ce rundunonin ’yansandan jihohi za su kasance masu kula da tabbatar da bin doka, wanzar da zaman lafiya da tsaro, kare rayuka da dukiyoyi, da kuma binciken laifukan da aka aikata a cikin jihohinsu.

Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ postsBio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Kotu Ta Yankewa Jami’an Tsaron Sa- Kai 3 Hukuncin Kisa A Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Majalisar Sarkin Musulmi Za Ta Kafa Bankin Musulunci Don Yaƙi Da Talauci
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    2027: Yadda Gwamnatin APC Ke Farautar Ƴan Adawa
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Ɗan Majalisa Zai Ɗauki Nauyin Biyan Ma’aikatan Da Gwamnatin Sakkwato Ta Riƙewa Albashi 

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Shirin Bayar Da Lamunin Gidaje Mara Kuɗin Ruwa A Kano
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Shirin Bayar Da Lamunin Gidaje Mara Kuɗin Ruwa A Kano

October 28, 2026
Kaduna Za Ta Mayar Da Yaran Da Ba Su Zuwa Makaranta 187,000 Makaranta Cikin Shekara 1
Ilimi

Kaduna Za Ta Mayar Da Yaran Da Ba Su Zuwa Makaranta 187,000 Makaranta Cikin Shekara 1

October 28, 2026
TUC Ta Yi Watsi Da Ƙarin Tallafin Sufuri Na ₦70,000, Ta Nemi A Biya Mafi ƙarancin Albashin ₦300,000
Manyan Labarai

TUC Ta Yi Watsi Da Ƙarin Tallafin Sufuri Na ₦70,000, Ta Nemi A Biya Mafi ƙarancin Albashin ₦300,000

October 28, 2026
Next Post
Abubuwan Da Ke Hana Yaran Arewacin Nijeriya Zuwa Makaranta

INEC Ta Fara Gyaran Rajistar Masu Zaɓe Bayan Zargin Amfani Da Hotunan AI

INEC Ta Fara Gyaran Rajistar Masu Zaɓe Bayan Zargin Amfani Da Hotunan AI

October 28, 2026
Zan Yi Wa Tinubu Kamfen Idan Ya Magance Matsalar Tsaro – Bafarawa

Zan Yi Wa Tinubu Kamfen Idan Ya Magance Matsalar Tsaro – Bafarawa

October 28, 2026
Babban Hafsan Sojojin Nijeriya Ya Goyi Bayan Kera Makamai A Cikin Gida Nijeriya

Babban Hafsan Sojojin Nijeriya Ya Goyi Bayan Kera Makamai A Cikin Gida Nijeriya

October 28, 2026
Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Jawo Hankalin Masu Zuba Jari Daga Ƙasashe 120

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Jawo Hankalin Masu Zuba Jari Daga Ƙasashe 120

October 28, 2026
Ban Taɓa Faɗin Mummunan Abu Kan El-Rufai Ba – Uba Sani

Ban Taɓa Faɗin Mummunan Abu Kan El-Rufai Ba – Uba Sani

October 28, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.