ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 31, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Daƙile Ƙwanton Ɓauna, Sun Ceto Makiyaya 2, Sun Ƙwato Dabbobi 520 A Sokoto

by Abubakar Sulaiman
22 hours ago

Rundunar haɗin gwiwa ta shiyyar Arewa maso Yamma, wato Operation FANSAN YAMMA, ta samu nasarori masu mahimmanci a fannin yaƙi da ta’addanci a jihohin Zamfara da Sokoto, inda suka fatattaki ƴan ta’adda, suka ceto mutane biyu, sannan suka dawo da dabbobi masu yawa da aka sace.

A cewar wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Kaptan Tamuno Sinivie, ya fitar, an gudanar da waɗannan ayyuka ne a ranar 28 ga watan Oktoba, 2026.

A Jihar Zamfara, jami’an Sector 2 da ke gudanar da sintiri na aiki a kan hanyar Anka zuwa Guruzu suka yi arangama da wani shirin kwanton ɓauna da ƴan ta’adda suka kafa a ɓangarorin biyu na titin. Duk da cewa wani soja guda ya samu raunin harbi yayin gumurzuzun, dakarun sun mayar da martani mai ƙarfi da jajircewa inda suka ci ƙarfin maharan, tare da tilasta musu tserewa da raunuka zuwa cikin daji da kuma dawo da cikakken zirga-zirga ga masu ababen hawa a kan hanyar.

ADVERTISEMENT

A wani farmakin daban da aka gudanar a ranar a Jihar Sokoto, takwarorin dakarun sun daƙile wani yunƙuri na ƴan ta’adda na satar dabbobi da sace makiyaya a ƙauyen Takasaba da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni.

Sakamakon bayanan sirri masu inganci, sojojin sun isa yankin da gaggawa inda suka tursasa wa maharan tserewa bayan musayar wuta, sannan suka yi nasarar ceto mutane biyu Malam Sulaiman mai shekaru 50 da Nasiru Sulaiman mai shekaru 14 tare da ƙwato dabbobi 520 da aka yi garkuwa da su, inda daga bisani suka miƙa waɗanda aka ceto ga hukumomin ƙaramar hukumar.

LABARAI MASU NASABA

Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin

Ɗan Takarar Gwamnan Sakkwato Na ADC, Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Da yake jawabi kan waɗannan nasarori, Kwamandan Rundunar Operation FANSAN YAMMA, Manjo Janar W.B. Idris, ya yaba da ƙwarewa da jajircewar da jami’an suka nuna a fagen daga, yana mai ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da kai wa ɓata-gari farmaki ba tare da sanyaya gwiwa ba.

Ya kuma sake jaddada aniyar sojojin na tabbatar da tabbataccen zaman lafiya, tare da yin kira ga al’umma da su ci gaba da ba da haɗin kai ta hanyar bayar da bayanan sirri na gaggawa ga jami’an tsaro domin ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin
  • Abubakar Sulaiman
    Ɗan Takarar Gwamnan Sakkwato Na ADC, Ya Tsallake Rijiya Da Baya
  • Abubakar Sulaiman
    Hukuncin Kotu Ne Zai Yanke Makomar Abdulsalam Gwarzo – INEC
  • Abubakar Sulaiman
    INEC Ta Tabbatar Da Pantami, Ta Ƙi Amince Wa Da Abdulsalam Gwarzo

MASU ALAKA

Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin
Labarai

Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin

October 31, 2026
Ɗan Takarar Gwamnan Sakkwato Na ADC, Ya Tsallake Rijiya Da Baya
Labarai

Ɗan Takarar Gwamnan Sakkwato Na ADC, Ya Tsallake Rijiya Da Baya

October 31, 2026
Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara
Manyan Labarai

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

October 30, 2026
Next Post
INEC Ta Tabbatar Da Pantami, Ta Ƙi Amince Wa Da Abdulsalam Gwarzo

INEC Ta Tabbatar Da Pantami, Ta Ƙi Amince Wa Da Abdulsalam Gwarzo

LABARAI MASU NASABA

Peng Liyuan Ta Yi Hira Da Uwargidan Shugaban Kasar Jamus

Peng Liyuan Ta Yi Hira Da Uwargidan Shugaban Kasar Jamus

October 31, 2026
Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin

Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin

October 31, 2026
Yadda Talauci Ya Sa Mutane Komawa Amfani Da Magungunan Gargajiya

Yadda Talauci Ya Sa Mutane Komawa Amfani Da Magungunan Gargajiya

October 31, 2026
Ɗan Takarar Gwamnan Sakkwato Na ADC, Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Ɗan Takarar Gwamnan Sakkwato Na ADC, Ya Tsallake Rijiya Da Baya

October 31, 2026
Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Yunkurin Dakile Kamfanonin Hada-hadar Sadarwa Na Kasar

Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Yunkurin Dakile Kamfanonin Hada-hadar Sadarwa Na Kasar

October 30, 2026
Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kasar Switzerland

Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kasar Switzerland

October 30, 2026
Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

October 30, 2026
Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Jamus

Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Jamus

October 30, 2026
Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

October 30, 2026
Sin Da Kasashen Afrika Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Taken Dunkule Harkokin Ciniki Da Zuba Jari A WTO

Sin Da Kasashen Afrika Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Taken Dunkule Harkokin Ciniki Da Zuba Jari A WTO

October 30, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.