Dakarun Operation Enduring Peace (OPEP) sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa ’yan banga hari tare da ƙone ofishinsu a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, Jihar Filato.
An kama waɗanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 1:40 na daren ranar 27 ga watan Oktoba, 2026, a yankin NEPA da ke Jos ta Arewa.
Mai magana da yawun OPEP, Kyaftin Chinonso Polycarp Oteh, ya ce ana tsare da waɗanda ake zargin domin ci gaba da gudanar da bincike.
Ya bayyana cewa kamen wani ɓangare ne na ƙoƙarin da sojoji ke yi na yaƙi da aikata laifuka da tabbatar da zaman lafiya a Jihar Filato.
Oteh ya buƙaci mazauna jihar su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen hana aikata laifuka da kama waɗanda ake zargi.













