’Yansanda a Jihar Kano sun kama wasu mutane biyu bisa zargin shirya sace hakimin ƙauyen Bangare da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa.
Waɗanda ake zargin su ne Aliyu Naziru Garba, mai shekara 20, da Bashir Alhasan, mai shekara 20.
An kama su ne bayan ’yansanda sun fara bincike kan barazanar da aka yi wa hakimin ƙauyen, Mallam Idris.
Mai magana da yawun rundunar ’yansandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce hakimin ya kai rahoton barazanar ofishin ’yansanda na Gezawa ranar 26 ga watan Oktoba.
Ya ce wani mutum ya kira hakimin da misalin ƙarfe 9:33 na dare, inda ya yi barazanar sace shi.
Hakan ya sa ’yansanda suka fara bincike wanda ya kai ga kama waɗanda ake zargin.
’Yansandan sun ce waɗanda ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa, yayin da ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.













