Bisa kididdigar da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Litinin 17 ga watan nan, daga watan Janairu zuwa watan Yuli na bana, an samar da kayayyaki yadda ya kamata, an wanzar da guraben ayyukan yi da farashin kaya, kana an samu karuwar cinikin waje, da ci gaban sabbin fannoni, kana tattalin arzikin Sin yana gudana yadda ya kamata, tare da samun sabon ci gaba da kyautatuwar tsarinsa baki daya.
Tun daga watan Janairu zuwa watan Yuli, yawan kudin da aka samu daga manyan masana’antun kasar Sin, ya karu da kashi 5.3 cikin dari, kana yawan hidimomin da aka samar a kasar ya karu da kashi 4.7 cikin dari, yayin da yawan kayayyaki da hidimomin da aka sayar ya karu da kashi 2.6 cikin dari, kuma yawan kudin kayayyakin da aka fitar zuwa kasashen waje da wadanda ake shigarwa kasar daga kasashen waje, ya kai yuan tiriliyan 30 da biliyan 126.4, adadin da ya karu da kashi 17.3 cikin dari.
Kakakin hukumar kididdiga ta kasar Sin Fu Linghui, ya bayyana a gun taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar a wannan rana cewa, a mataki na gaba, za a kara bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima, da sa kaimi ga raya sabbin sana’o’i, da fadada bukatun cikin gida, da kyautata tsarin samar da kayayyaki, ta yadda hakan zai tabbatar da kyautata zaman rayuwar jama’a, da inganta karfin samun ci gaba da raya al’ummar kasar, da kuma sa kaimi ga raya tattalin arziki mai inganci yadda ya kamata.(Zainab Zhang)














