ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 31, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Ayyana Zaman Makokin Kwanaki 3 Domin Jimamin Mutanen Da Suka Rasu a Hatsarin Jirgin NAF

by Sadiq
4 weeks ago

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki na ƙasa saboda jami’an Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) da suka rasu a hatsarin jirgin soji a Jihar Ondo.

Ya kuma bayar da umarnin sauke tutocin Nijeriya zuwa rabi a faɗin ƙasar domin girmama jami’an da suka rasa rayukansu.

Jirgin NAF ƙirar ATR-42 ya yi hatsari a kusa da wani sansanin sojin ruwa da ke Igbokoda, Jihar Ondo, yayin da ya taso daga Benin, Jihar Edo, zuwa Legas.

ADVERTISEMENT

Jirgin yana ɗauke da fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin guda bakwai a lokacin da ya yi hatsari.

Tinubu ya bayyana hatsarin a matsayin babban rashi ga rundunar soji da kuma ƙasar baki ɗaya.

LABARAI MASU NASABA

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

Ya ce ba za a manta da sadaukarwar jami’an tsaron da ke sadaukar da rayukansu wajen kare Nijeriya ba.

Shugaban ya umarci Rundunar Sojin Sama ta gudanar da bincike cikin gaggawa domin gano musabbabin hatsarin da kuma ɗaukar matakan hana faruwar irin wannan abu a nan gaba.

Ya kuma yaba wa rundunar bisa fara aikin neman waɗanda abin ya shafa da ceto su nan take bayan aukuwar hatsarin, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

MASU ALAKA

Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara
Manyan Labarai

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

October 30, 2026
El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci
Manyan Labarai

El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

October 30, 2026
An Tsare Ɗan TikTok Kan Zargin Ɓata Sunan Jami’an KAROTA
Manyan Labarai

An Tsare Ɗan TikTok Kan Zargin Ɓata Sunan Jami’an KAROTA

October 30, 2026
Next Post
ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

ADC Da Atiku Sun Zargi Gwamnatin APC Da Yin Watsi Da Jin Daɗin Malamai

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Yunkurin Dakile Kamfanonin Hada-hadar Sadarwa Na Kasar

Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Matakin Amurka Na Yunkurin Dakile Kamfanonin Hada-hadar Sadarwa Na Kasar

October 30, 2026
Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kasar Switzerland

Shugaba Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kasar Switzerland

October 30, 2026
Jami’an Tsaro Sun Kashe Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane, Maidawa Da Wasu A Kwara

Mutane 3 Sun Ƙone Kurmus Yayin Da Wata Bas Ta Yi Karo Da Babbar Mota A Kwara

October 30, 2026
Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Jamus

Shugaba Xi Ya Zanta Da Shugaban Jamus

October 30, 2026
Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci

October 30, 2026
Sin Da Kasashen Afrika Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Taken Dunkule Harkokin Ciniki Da Zuba Jari A WTO

Sin Da Kasashen Afrika Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Taken Dunkule Harkokin Ciniki Da Zuba Jari A WTO

October 30, 2026
Kasar Sin Ta Gabatar Da Samfuran Taurarin Dan Adam Na Fengyun Masu Fasahar AI

Kasar Sin Ta Gabatar Da Samfuran Taurarin Dan Adam Na Fengyun Masu Fasahar AI

October 30, 2026
Bikin CIIE Dama Ce Ga Najeriya

Bikin CIIE Dama Ce Ga Najeriya

October 30, 2026
El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

El-Rufai Ya Shafe Kwanaki 256 A Tsare, Ya Nemi A Yi Masa Adalci

October 30, 2026
Kwamitin Koli Na JKS Ya Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Tare Da Wadanda Ba ’Yan JKS Ba

Kwamitin Koli Na JKS Ya Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Tare Da Wadanda Ba ’Yan JKS Ba

October 30, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.