Phrank Shaibu, babban hadimin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya tafk Makka domin yi wa kansa addu’a maimakon yi wa Nijeriya.
Shaibu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today ranar Litinin, inda ya bayyana ziyarar Tinubu ta Umrah a matsayin “ziyarar ibada mai alaƙa da siyasa”.
Ya kuma soki shugaban ƙasar kan kalaman da ya yi na cewa ya samu hikimar da yake buƙata wajen jagorantar Nijeriya da kuma goyon bayan addini domin neman wa’adi na biyu.
Shaibu ya nuna shakku kan gaskiyar imaninsa, inda ya yi nuni da ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir el-Rufai.
Ya ce Tinubu na da ikon taimakawa wajen ganin an sake shi.
Ya kuma danganta batun da matsin tattalin arziƙin da ake fuskanta a Nijeriya, yana mai cewa al’umma da dama na shan wahala wajen samun abinci.
Haka kuma, Shaibu ya yi iƙirarin cewa Atiku ne ya ɗauki nauyin Tinubu na zuwa Makka na farko da ya yi a rayuwarsa, sannan ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya taɓa shafe kwanaki 30 a Makka a watan Ramadan ba tare da ya sanar da jama’a ba.
Tinubu ya bar Abuja zuwa Makka a ranar 29 ga watan Oktoba domin gudanar da ibadar Umrah.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya ce ziyarar dama ce ga shugaban ƙasar na yin addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Nijeriya.
Bayan kammala ibadar Umrah, Tinubu ya ce ya yi Nijeriya da al’ummarta addu’a.














