Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace ɗaliban makarantar Islamiyya 14 a garin Pandogari, da ke Ƙaramar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.
An sace ɗaliban ne ranar Asabar yayin da suke taimaka wa malaminsu yake girbin masara a gonarsa da ke ƙauyen Tungan-Bako.
Maharan sun kuma yi awon gaba da malamin.
Mai magana da yawun rundunar ’yansandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin, inda ya ce ɗalibai 14 aka sace, ba 50 ba kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.
Ya ce jami’an tsaro sun fara ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.
A wani labarin kuma, Jonathan Vatsa, mai magana da yawun ɗan takarar gwamnan Jihar Neja na jam’iyyar SDP, ya soki Gwamna Mohammed Bago kan taɓarɓarewar tsaro a jihar.
Vatsa ya zargi gwamnan da mayar da hankali kan zaɓen gwamna na 2027 maimakon magance matsalar tsaro da kare rayukan al’umma.
Ya kuma yi zargin cewa jami’an tsaro a jihar ba su da isassun motocin aiki da kayan aikin da za su taimaka musu wajen yaƙi da hare-haren ’yan bindiga.
A wani lamarin daban kuma, wasu ’yan bindiga sun sace mutum shida da suka taso daga Kano zuwa Jihar Benue domin kai gawar wata mata da ta rasu.
Rahotanni sun ce maharan sun tare motarsu a kan hanyar Adoka, suka yi awon gaba da mutanen shida, sannan suka bar gawar matar a bakin hanya.













