Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya ce Shugaba Bola Tinubu zai kayar da Atiku Abubakar da Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, ko da kuwa ‘yan takarar biyu sun haɗa kai.
Fayose ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.
Ya ce Atiku da Obi za su fuskanci ƙalubale mafi girma idan kowanensu ya tsaya takara shi kaɗai, saboda hakan zai raba ƙuri’un magoya bayansu.
Tsohon gwamnan ya kuma yi iƙirarin cewa yankin Kudu maso Yamma zai bai wa Tinubu gagarumin rinjaye, sannan ya ce yana sa ran shugaban zai samu aƙalla kuri’u miliyan 12.
Fayose, wanda Tinubu ya naɗa matsayin shugaban hukumar samar da wutar lantarki a karkara (REA), ya kuma kare manufofin tattalin arziƙin shugaban.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta samu ci gaba wajen farfaɗo da tattalin arziƙi da kuma inganta ababen more rayuwa, ciki har da hanyoyi.
Kalaman Fayose na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar yin haɗaka da tsayar da ɗan takara guda ɗaya a zaɓen 2027.














