Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 10 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Katsina.
An yi garkuwa da mutanen ne a ƙauyukan Unguwan Daudu da Unguwan Chibauna da ke ƙaramar hukumar Funtua.
Rundunar sojin ta ce sojojin da ke aiki a yankin Sabuwa sun samu bayanan sirri kan satar mutanen, inda suka bi bayan ‘yan bindigar.
A yayin da sojojin ke bin su, ‘yan bindigar sun tsere zuwa cikin daji, inda suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.
Waɗanda aka ceto sun haɗa da maza uku, mata shida da jariri.
Sojojin sun ce an kai waɗanda aka ceto waje mai tsaro, kuma za a miƙa su ga hukumomin ƙaramar hukumar Sabuwa domin duba lafiyarsu da kuma mayar da su cikin iyalansu.
Aikin na daga cikin ƙoƙarin da sojojin ke yi na daƙile ayyukan ‘yan ta’adda da kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a yankin Arewa maso Yamma.














