Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ce bai kamata gwamnati ta riƙa kashe kuɗaɗen jama’a wajen ayyukan addini, ciki har da yi wa jama’a aure da aikin hajji ba.
Melaye ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin KAA Truths podcast.
Jigon na jam’iyyar ADC ya soki gwamnatocin tarayya da jihohi kan kashe maƙudan kuɗaɗe wajen ayyukan addini, maimakon amfani da kuɗaɗen wajen gyaran hanyoyi, asibitoci da sauran muhimman ababen more rayuwa.
Ya ce, “Gwamnati ba ta da alhakin ɗaukar nauyin ayyukan addini, ciki har da aure. Ba daidai ba ne gwamnati ta riƙa ɗaukar nauyin addini.”
Melaye ya kuma tambayi dalilin da ya sa gwamnati ke kashe biliyoyin Naira wajen ɗaukar nauyin mutane zuwa Makka da Kudus, alhali ƙasar na fama da matsalolin hanyoyi da rashin ingantaccen kiwon lafiya.
Ya ce kamata ya yi a ɗauki addini a matsayin wani lamari na mutum, yayin da kuɗaɗen gwamnati su mayar da hankali kan ayyukan ci gaban ƙasa.














