Wani shirin hadin gwiwa tsakanin hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da raya al’adu ta MDD (UNESCO) da dandalin Codemao na kasar Sin, mai koyar da ilimin sarrafa fasahohi ko Coding, na samun nasara wajen shigar da ilimin fasahar AI cikin makarantun da ke fadin nahiyar Afrika.
A cewar Mary Nyasimi, kwararriyar mai tsara shiri a ofishin UNESCO da ke gabashin Afrika, AI da fasahohin dijital na sauya tsarin koyo da koyarwa a fadin nahiyar Afrika, inda suke samar wa dalibai muhimman dabarun da za su amfane su a nan gaba a bangarorin sana’o’i da kirkire-kirkire.
Shirin na koyar da matasa ilimin sarrafa fasahohi ko Coding, wanda UNESCO da Codemao suka kaddamar a shekara ta 2021, na da nufin samar da ilimin fasahar AI da na Coding, mai aminci bisa daidaito da tafiya tare da kowa, a fadin nahiyar Asiya da Afrika.
A cewar jami’ar, tsakanin shekarar 2021 da 2022, sama da malamai 200 daga kasashen Jamhuriyar Congo da Kenya da Namibia da Thailand, da suka hada da kaso 45 na mata, sun kammala shirin UNESCO na kasa da kasa na farko, na karbar horo kan Coding.
Ta kara da cewa, shirin na amfani ne da dabarar koyar da mai koyarwa, inda sabbin malamai da aka horar suke koyar da dubban takwarorinsu da dalibai ilimin fasahohin Coding da dijital, a fadin nahiyar. (Fa’iza Mustapha)














