• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wa Suka Fi Cancanta A Nada Ministocin Tinubu?

by Aisha Seyoji
2 years ago
Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 

Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri

A halin yanzu ‘Yan Nijeriya na ta dakon ganin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada ministocitoci. Shin a ganinka/ki, wane ne mafi cancanta a nada shi Minista daga Jiharku. Fadi suna da kuma takaitaccen bayani kan zabin naka ko naki.

LUKMAN B. ADAM: Pantami Ya Fi Cancanta Daga Gombe

A jiharmu ta Gombe kam gaskiya babu wanda ya cancanta daya wuce Prof Isa Ali Ibrahim Pantami. Domin kuwa shi ne kadai ya san damuwan talakawa kuma yake taimaka musu sannan kuma Mutum ne wanda ba ya kyamar mutane ga kuma ilimi ta kowane bangaren rayuwa da Allah ya ba shi kuma sannan ga shi ya yi mun gani duk Nijeriya tunda ake ba a taba yin Minista da ya yi aikin da ya yi ba.

Kai a takaice dai Nijeriyar ma kanta irin Prof Isa Ali muke bukata ba ‘yan bulkara da karya da rainin hankali ba.

CMRD MOHD GADDAFI AWWAL: El-Rufai Ya Kamata A Nada Daga Kaduna

Gaskiya ni dai a nawa ra’ayin, Malam Nasiru El-Rufai ya fi cancanta a nada daga Kaduna, jajirtacce ne kowa ya san shi, ba ya wasa a kan aikinsa.

SADEEK RUFAI DANGUGUWA: Ina So A Dauki Kwankwaso Daga Kano

Ina son Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso na Jahar Kano ya kasance daya daga cikin Ministocin da za a nada. Ba don komai ba, sai don kyakkyawan yakinin da nake dashi a kansa, saboda Kwankwaso mutum ne mai sanin makamar aiki ta kowacce siga, ba zan riya cewa Kwankwaso ya kai makura ba, domin kaiwa makura siffa ce da Ubangiji Ya kabance kanshi da ita, amma tabbas Kwankwaso na da dukkan ‘Capacity’ din zama daya daga cikin Ministocin kasar nan.

JAFAR S. HASSAN KARABA: Gwamma A Nada Sani Sha’aban A Kaduna

Mu a Kaduna wanda nake ganin ya fi kowa cancanta a nada shi shi ne Sani Sha’aban, shi muke so, saboda ya fi Nasiru sanin hakkin al’umma wallahi.

IT’Z JAMEEL MOHD: Ba Ruwanmu Da Wani Minista, Fatanmu Farashin Kayan Masarufi Ya Sauka

Kullum fata muke farashin kayan masa rufi ya yi kasa talaka ya ji dadi a Nijeriya. Babu ruwanmu da wani minister. Buhun masara 48k, Shinkafa 35k, Litar Mai 600, Ina talakan Nijeriya zai sa kansa?

APC Change Change: Ganduje Da Gawuna Muke So A Nada Daga Kano

A gaskiya mu dai a ganinmu babu wanda ya cancanta a nada a matsayin minister daga Jihar Kano illa Ganduje da Gawuna.

ABDUL’AZIZ MOHAMMED: Allah Ya Zaba Mana Mafi Alheri Daga Gombe

Da farko dai ina miki barka da wannan lokaci, Allah ya datar da mu amin. Ni dai a nawa bangaren a gaskiya addu’a nake, duk wanda zai zama alkhairi ga al’ummar Jihar Gombe da ma kasa gaba daya Allah ya tabbatar mana da shi amin.

ALIYU SULAIMAN: A Nada Mana Isah Yuguda Daga Jihar Bauchi

Ni dai nawa zabin a Jihar Bauchi shi ne: Isah Yuguda. Sabida a Bauchi babu wanda bai san Jarumtarsa ba. A lokachin Isah Yuguda a Bauchi, ‘Principal’ din ‘Secondary school’ ma na hawa mota. Amma ban da zamanin Bala. Ya yi minista a baya na ‘abiation’, an ga rawar da ya taka. Yanzu ma idan ya samu dama, zai sake yin abin da ya saba. Sabida shi dan mai kishin mutanensa ne a zuciya.

UMAR ABDULLAHI: Allah Ya Sa A Nada Mana Hazikai

Ina miki fatan alkhairi, Allah ya sa mu dai a sa mana hazikai masu aikin da aka nada su wanda za mu ga canji na alkhairi a kasarmu Nijeriya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 
Ra'ayoyi

Madallah Da Hutu Ga ‘Yan Sakandire Domin Azumi 

March 18, 2025
Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri
Ra'ayoyi

Ya Kamata A Biya Yaran Da Aka Gurfanar Saboda Zanga-Zanga Cikakkiyar Diyya – Ajiyan Yawuri

November 10, 2024
Nijeriya
Ra'ayoyi

Ra’ayoyin ‘Yan Nijeriya A Kan Zagayowar Ranar Samun ‘Yancin Kai

October 5, 2024
Next Post
Manoman Tumatur 70,000 Na Bukatar Tallafin Gwamnatin Kano – Yadakwari

Manoman Tumatur 70,000 Na Bukatar Tallafin Gwamnatin Kano - Yadakwari

LABARAI MASU NASABA

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Triumph

Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.