“Mataki ne mai burgewa”, in ji Miriam Akpan, ma’aikaciyar gwamnati a Nijeriya wadda ta nuna yabo ga layin dogo na Abuja bayan da ta hau jirgin, layin dogon da aka kaddamar da ita a hukumance a kwanan baya. Miriam Akpan ta ce, “Jirgin yana da dadi, kuma an tafiyar da tashoshin jirgin yadda ya kamata. Yanzu kudin da na kashe wajen zirga-zirga tsakanin gida da ofis ya ragu sosai, ga shi kuma jirgin ya fi sauri idan an kwatanta da mota wadda ta kan samu cunkuso, gaskiya na ji dadi.”
Mustapha Bello, dalibi ne daga jami’ar Abuja, wanda shi ma ya ji dadin tafiya ta layin dogon, ya kuma yi fatan za a fadada layin dogo har zuwa bayan garin da yake zama, ya ce, “tafiya ce mai dadi, kuma ina fatan layin dogon zai taimaka ga saukaka harkokin zirga-zirga ga mazauna birnin, baya ga kyautata tattalin arziki da zaman al’umma.”
- An Tafka Gumurzu, Sojoji Sun Kashe Ƴan Boko Haram Da Yawa, Wasu Sun Miƙa Wuya
- Sadaukar Da Kai Ga Hidimtawa Jama’a: Tasirin Mahaifin Xi Jinping A Kan Dansa
Kamfanin kasar Sin ne ya gina layin dogon na Abuja, wanda ya kasance layin dogo na farko da aka shimfida a birnin, wanda kuma ya kasance wata babbar nasara da aka samu sakamakon aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”. An ce, layin dogon na da tsawon kilomita 45, kuma bayan da aka kaddamar da shi a hukumance, zai yi matukar saukaka matsalar cunkuson mota da ake fuskanta a birnin, wanda baya ga hakan, zai kuma rage kudin zirga-zirga ga mazauna birnin, tare da bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma a sassan da layin dogon ya ratsa, wanda har zai haifar da babban tasiri ga bunkasuwar layukan dogo a biranen kasashen yammacin Afirka da ma na Afirka baki daya.
Hasali ma dai, cikin shekaru 10 da aka gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, kasar Sin ta daddale takardun yarjejeniyoyin hadin gwiwa sama da 200 tare da kasashen duniya sama da 150 da ma kungiyoyin kasa da kasa fiye da 30, shawarar da ta samar da dandalin hadin gwiwa mafi girma a tsakanin kasa da kasa, wadda kuma ta samar da hakikanan alfanu ga jama’ar kasashen da suka karbi shawarar, kuma layin dogo na Abuja wani misali ne kawai na nasarorin da aka cimma sakamakon aiwatar da shawarar.
Duk da haka, ko irin wannan hadin gwiwar da ke haifar da alfanu ma Amurka da sauran kasashen yamma na shafa masa bakin fenti, inda shugaban kasar Amurka Joe Biden a yayin da ya tattauna tare da dan jarida a kwanakin baya, ya bayyana shawarar a matsayin “shirin da ake kyamarsa”, ya kuma kara da cewa, “A duba me ke faruwa a Afirka”.
Haka ne, a duba me ke faruwa a Afirka. Sakamakon shawarar “ziri daya da hanya daya”, kasashen Afirka da dama sun samu tagwayen hanyar mota ta farko, da ma gadar ketare teku ta farko da ma yankin masana’antu na farko, baya ga cibiyar kandagarkin cututtuka mai ingantattun kayayyakin aiki ta farko da ta game ko ina a nahiyar Afirka, da gaske ne shawarar ta samar da manyan sauye-sauye ga kasashen Afirka.
Sinawa kan ce, sai wanda ya sa takalma ya san ko ta dace ko a’a. Abin hakan yake, sai kasashen da suka aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya suke iya magana a kanta. Shugaban tarayyar Nijeriya Bola Tinubu a yayin da ya halarci bikin kaddamar da layin dogon, ya bayyana shi a matsayin “hanya mai kyakkyawar makoma da za ta taimakawa Nijeriya inganta ababen zirga-zirga da ma bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma”, da kuma “alama ta dauwamammen ci gaban Nijeriya”, furucin da ya bayyana ma’anar shawarar ga kasashen da suka karbe ta.
Abu ne mai sauki a yi wa wasu suka, sai dai, da wuya a iya yin wani abu da ya zarce na wasu kyau. Kasar Sin na son ganin kasa da kasa su aiwatar da hadin gwiwar cin moriyar juna tare da kasashen Afirka cikin daidaito, don su samar da hakikanin taimako ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al’umma na kasashen Afirka. Muna kuma fatan ganin Amurka ta samar da kudaden jari, don ta samar da hakikanin gudummawa wajen raya kasashen Afirka. (Mai Zane:Mustapha Bulama)