A yau Talata, 20 ga Oktoba, za a fafata tsakanin Paris Saint-Germain...
Read moreDetailsAbubuwa 3 Da Za Su Sa Ɗan Wasa Ya Lashe Kyautar Ballon...
Read moreDetailsKofin Duniya Na Mata ’Yan Ƙasa Da Shekaru 17: Koriya Ta Kudu...
Read moreDetailsƘungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Paris Saint-Germain (PSG) ta tabbatar da...
Read moreDetailsHukumar Kwallon Kafa ta Saudiyya ta dage wasanni uku na gasar Saudi...
Read moreDetailsMataimakin kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray, Ismael García, ya bayyana cewa...
Read moreDetailsƘungiyar ƙwallon ƙafa ta Plateau United ta samu gagarumar nasara bayan ta...
Read moreDetailsTawagar kwallon kafa ta Nijeriya tana mataki na biyu a rukuni na 12 a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a 2027. Hakan ya biyu bayan da Guinea Bissau ta doke Super Eagles 3-0 a wasan cikin rukuni a satin da ya gabata a filin wasa na Estádio Nacional 24 de Setembro. Kawo yanzu, da wannan sakamakon Guine Bissau ce ta daya a kan rukuni na 12 da maki shida, bayan da ta fara nasara a kan tawagar kasar Tanzaniya 2-0 a wasan farko a rukunin. Ita kuwa Nijeriya tana da maki uku, saboda doke Madagascar 2:1 a wasan farko da ta yi a Uyo, yayin da Madagascar da Tanzaniya suke da maki daya kowwacce. Me wannan rashin nasara da Super Eagles ta yi a Guinea Bissau ke nufi? Mai koyar da ‘yanwasan tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Eric Chelle ya bayyana cewa daga dalilan da ya sa suka yi rashin nasara har da rashin fili mai kyau da suka buga da Guinea Bissau da kuma rashin kyawun yanayi, sai dai ya ce ba su taka rawar da ya kamata su samu maki ba a fafatawar. Rabon da Super Eagles ta yi rashin nasara da aka zura mata kwallaye da yawa tun wasan sada zumunta da Portugal da yi rashin nasara 4:0 ranar 17 ga watan Nuwambar 2022. Kafin nan kuma Sifaniya ta doke Nijeriya 3:0 ranar 23 ga watan Yuni a 2013 a FIFA Confederation Cup. Kenan ba kasafai ake zura kwallaye da yawa a ragar Super Eagles ba, amma mai ya sa Guinea Bissau ta yi wannan namijin kokarin. A tarihin karawar tsakanin kasashen biyu, Guinea-Bissau ta samu nasara daya a wasannin baya, yayin da Nijeriya ta ci fafatawa uku cikin karawa hudu da suka gabata, kafin wannan da suka kara a Guinea Bissau. A wasan neman gurbin AFCON na 2023, Guinea-Bissau ta ci Nijeriya 1:0 a Abuja, kafin Super Eagles ta rama da ci 1:0 a Bissau. Rashin nasarar da Nijeriya ta yi a wannan karawar ya sa za ta sake shiga cikin matsi a wasannin da suke gabanta, domin neman gurbin AFCON 2027. Amma masana na ganin irin wannan sakacin ne ya sa Super Eagles ta kasa samun gurbin shiga gasar kofin duniya da aka yi a Amurka da Kanada da Medico, duk da cewar kasashe 10 ne ta wakilci Afirka a babbar gasar kwallon kafa ta duniya. Za a gabatar da gasar cin kofin Afirka tsakanin kasashe uku da suka hada da Kenya da Uganda da kuma Tanzaniya a shekarar 2027. Rukuni na 12 ya kunshi Guine Bissau da Nijeriya da Tanzani da kuma Madagascar kenan tun da mai masukin baki tana cikin rukunin kenan kasa daya ce ba za ta samu tikitin shiga wasannin ba a cikin rukunin. Kenan duk wadda ta kammala wasaninta da maki mafi rinjaye, ita ce za ta je babbar gasar kwallon kafa ta Afirka da za a yi a badi a 2027. Ita Tanzani da take mai masaukin baki tana cikin wannan rukunin ne, domin ta samu damar hada yan kwallon da za su taka mata rawa a wasannin badi.
Read moreDetailsRa’ayin mutane ya banbanta musamman a kan takaddamar da ake yi ko kuma ta bullo tsakanin danwasa Cristiano Ronaldo da kociyan tawagar ‘yanwasan Portugal, Jorge Jesus. Sai dai magoya bayan Portugal sun fara ganin yadda tawagar ta buga wasa ba tare da Cristiano Ronaldo ba, bayan da kasar ta doke Denmark da ci 4-2 a gasar Nations League ranar Alhamis. Joao Cancelo da Goncalo Ramos ne suka bai wa bakin damar cin kwallo biyu, yayin da Mikkel Damsgaard da Rasmus Hojlund suka farke wa Denmark. Tsohon dan wasan Manchester United, Hojlund, ya yi murnar cin kwallon da ya ci da kwaikwayon salon yadda Ronaldo ke yi 'Siuuu' da zarar Ronaldo ya zura kwallo a raga - kuma wannan ne karo na biyu da Hojlund ya yi irin haka a wani lokaci da suka fafata da Portugal. dan wasa bitinha ne ya sake ci wa Portugal kwallo ta uku, sannan Joao Felid ya kara ta hudu a wasan da aka buga a birnin Copenhagen, kuma sakamakon ya bai wa Portugal damar samun maki uku. Kuma wannan ne karon farko da Portugal ta buga wasa tun bayan da Ronaldo mai shekara 41, wanda shi ne mafi zura kwallaye a tarihin kwallon kafar kasashe, ya bar sansanin kasar, bayan an ajiye shi a benci a wasan da suka yi da Norway. Bayan nasarar da suka samu a Denmark, kociyan tawagar ta Portugal, Jorge Jesus, mai shekaru 72 ya ce: "Akwai ‘yan wasa masu matsayi na musamman. Wannan abu ne a fili. Ya ci gaba da cewa "Amma zan sake fada - ka'idojin iri daya ne ga kowa. Wannan ita ce hanyar da na bi a duk tsawon aikina na horarwa, kuma zan ci gaba da bin ta." Sai dai a daren ranar da kociyan ya yi wannan maganar 'yar uwar Ronaldo, Elma Abeiro, ta rubuta a shafukan sada zumunta tun da farko cewa: "Cin amana abinci ne da aka fi jin dadinsa idan aka ci shi a hankali.’ Duk wanda yake bibiyar wasannin kwallon kafa ya san da cewa an shafe shekaru ana ganin kamar ba za a iya cire Ronaldo daga cikin tawagar ba bayan da ya ci wa Portugal kwallo 146 a wasanni 234. Sai dai a shekarun baya da kokarinsa ya ragu, an fara cece-kuce cewa watakila dan wasan Al-Nassr, wanda ya ci kwallo 979 jimilla a rayuwarsa ta kwallon kafa, yana hana tawagar yin abin da ya dace. ”Idan Na Yi Laifi A Hukunta Ni” - Ronaldo Cristiano Ronaldo ya ce bai yi ritaya daga buga wa tawagar Portugal wasanni ba, amma ya amince cewa ya kamata a hukunta shi saboda barin sansanin da suke sauka ba tare da izini ba. Kyaftin din mai shekara 41 ya bar sansanin Portugal bayan da ya kasance a benci ba tare da an yi amfani da shi ba a wasan da suka yi da Norway, sannan ya gano cewa ba zai fara karawa da Denmark ba a gasar Nations League. Ronaldo mai buga wasa a Al-Nassr, ya ci kwallo 146 a wasa 234 da ya buga wa Portugal, tare da taimaka wa kasar wajen lashe Euro 2016 da gasar Nations League sau biyu a tarihi. ...
Read moreDetailsShugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), Patrice Motsepe, ya bayyana cewa...
Read moreDetails© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.