Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Plateau United ta samu gagarumar nasara bayan ta doke abokiyar karawarta Kano Pillars da ci 4-0 a wasan mako na takwas (Matchday 8) na Gasar Firimiya ta Nijeriya (NPFL), da aka fafata a Sabon Filin Wasa na (New Jos Stadium) a ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoba, 2026.
Ƙungiyar ta Plateau United, wadda aka fi sani da “Peace Boys”, ta fara wasan da ƙaimi inda ɗan wasanta Paul Samson ya zura ƙwallo ta farko a raga tun a minti na uku (3) da fara wasa. Ana gab da tafiya hutun rabin lokaci, a ƙarin lokacin da aka bayar (45+), Ekundayo Ojo ya ninka ƙwallayen zuwa 2-0.
A zagaye na biyu, Plateau United ta ci gaba da matsa lamba inda Samuel Ayanrinde ya ci ƙwallo ta uku a minti na 82. Kafin a tashi daga wasan, ɗan wasa Nenrot Silas ya buga bugun fenareti da ya shiga raga a minti na 90+4, lamarin da ya kawo ƙarshen fafatawar da ci 4-0.
Wannan gagarumar nasara ta bai wa Plateau United damar farfaɗowa daga shan kashin da ta yi a makon da ya gabata da ci 2-0 a hannun Enyimba United. Da wannan sakamako, ƙungiyar ta haura zuwa matsayi na uku a teburin gasar NPFL da maki 14, tazarar maki uku kacal tsakaninta da Rangers International da ke jagorancin teburin.
A ɓangare guda, wannan rashin nasara ta zama babban koma-baya ga ƙungiyar Kano Pillars, wadda ta kasa tabuka wani abin a-zo-a-gani a wannan karawa a waje, yayin da Plateau United ke shirin fuskantar ƙungiyar Sporting Lagos a wasanta na gaba a mako mai zuwa.














