ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi: Akwai Bukatar Mayar Da Shekara Ta 2026 Ta Zama Muhimmiyar Shekara Ga Dangantakar Sin Da Amurka

by Sulaiman
4 months ago
Xi

Da safiyar yau Alhamis 14 ga watan nan na Mayu, a babban zauren jama’a na birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin.

Xi ya nuna cewa, a halin yanzu ana ci gaba da fuskantar sauye-sauye da ba a taba gani irinsa ba a karnin da ya gabata, kuma yanayin kasa da kasa yana cikin rudani da sauye-sauye. Shin ko Sin da Amurka za su iya wuce “tarkon Thucydides”, wato ra’ayin bunkasar wata kasa mai tasawo ta yi takara da maye gurbin wata kasa mai wadata? Kuma ko za su iya kirkiro sabon salo na dangantakar manyan kasashe? Shin ko za su iya hada kai don fuskantar kalubalen duniya, da kuma samar da karin kwanciyar hankali ga duniya tare? Shin ko za su iya yin la’akari da jin dadin al’ummomin kasashen biyu, da makomar bil’adama cikin hadin gwiwa don bude kyakkyawar makoma ga dangantakar kasashen biyu?

Wadannan tambayoyi ne na tarihi, da duniya da kuma jama’a suke shakka, kuma suna cikin tambayoyin da shugabannin manyan kasashe ke bukatar su ba da amsa tare.

ADVERTISEMENT

Xi ya jaddada cewa, muradun bai daya tsakanin Sin da Amurka sun fi muhimmanci fiye da sabanin ra’ayi, kuma nasarar kowannensu dama ce ga juna, kana kwanciyar hankali a dangantakar Sin da Amurka yana amfanawar duniya. Ya kamata bangarorin biyu su zama abokan hadin gwiwa maimakon abokan hamayya, su kuma taimaki juna da samun ci gaba tare, da kuma bin hanyar da ta dace tsakanin manyan kasashe a sabon zamani. Xi yana mai fatan yin hadin gwiwa da shugaba Trump, don aiwatar da musayar ra’ayi kan manyan batutuwan da suka shafi kasashen biyu da kuma duniya, tare da jagorantar bunkasar dangantakar Sin da Amurka yadda ya kamata, don mayar da shekara ta 2026 ta zama shekara mai muhimmanci a tarihi ga samun kyakkyawar bunkasar dangantakar Sin da Amurka.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce yana fatan gudanar da babbar tattaunawa tare da shugaba Xi Jinping. A cewarsa, “Akwai wadanda ke ganin wannan ne taro mafi girma da aka taba gudanarwa. Duk da cewa mun fuskanci wahalhalu, amma za mu kamo bakin zaren. Za mu kai ga cimma kyakkyawar makoma tare.”

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

A kalaman nasa, Trump ya nanata kiran shugaba Xi da babban jagora. Yana mai cewa “Ina alfahari da kasancewa abokinka, kuma alaka tsakanin Sin da Amurka za ta ci gaba da inganta sama da lokutan baya.”

Bugu da kari, a yau Alhamis 14 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump suka ziyarci wurin ibada na Tiantan tare.

Xi, ya yi maraba da Trump a babban ginin Qiniandian, sun kuma dauki hoto tare a filin da ke gaban babban ginin wurin ibadar, daga nan kuma suka kewaya cikin babban ginin tare.

Xi
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
Daga Birnin Sin

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Next Post
Sin Na Fatan Raya Huldar Sin Da Amurka a Sabon Matsayi Tare Da Amurka

Sin Na Fatan Raya Huldar Sin Da Amurka a Sabon Matsayi Tare Da Amurka

LABARAI MASU NASABA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.