ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Taron AI Na Duniya: Kaya Ya Kwance A Tushen Kaba

by Sulaiman and CGTN Hausa
2 months ago
AI

Iyaye da sauran jagororin al’umma sun kasance masu nuna damuwa sosai da yanayin karuwar hadurran da ake fuskanta dangane da amfani da fasahohin zamani, saboda mummunan tasirin da suke yi ga tushen rayuwa, kana a sa’i daya kuma, kusan dukkan al’ummomi suna fargabar irin halin da za a shiga matukar ba a sanya ka’idoji na hana amfani da fasahohin ta hanyar da ba ta dace ba.

Lura da ire-iren wadannan abubuwa masu cin tuwo a kwarya da kuma yadda ake samun saurin karuwar barazanar rashin daidaita hanyoyin amfani da fasahohin zamani, a kwanan nan, sassan kasa da kasa sun amince da kafuwar kungiyar hadin gwiwa kan fasahar kirkirarriyar basira (AI) ta duniya mai lakabin WAICO a takaice, wacce za ta yi kokarin samar da sahihin kawance na bunkasa fasahar ta AI mai amfanarwa da kuma tunkarar kalubalen rashin tabbas a bangaren kula da sha’anin fasahar.

Wannan sabuwar nasara da aka cimma a taron da ya gudana a birnin Shanghai na kasar Sin, ta kasance tamkar share hawaye ga masu fargabar mummunan tasirin fasahohin zamani, ciki kuwa har da yawaita amfani da su ba bisa ka’ida ba ta fuskar soji da sauran miyagun laifuffuka. Ta hanyar kungiyar WAICO, mabambantan bangarori za su hada karfi da karfe wajen tsara kyawawan manufofi da ka’idojin da za su hana fasahohin na zamani lalata ginshikin zamantakewa da kuma samar da ci gaba mai ma’ana ba na mai hakar rijiya ba.

ADVERTISEMENT

A kokarinta na sauke nauyin da ke wuyarta a matsayin babbar kasa a duniya, kasar Sin ta bakin shugaba Xi Jinping ta ba da shawarar bin ka’idar gudanar da al’amura a fili, da hadin gwiwar samun nasara ga dukkan bangarori, da bai wa juna sabbin fasahohi na zamani da bunkasa ci gaban sashen masana’antu mai amfani da fasahar AI. Ko da yake, masu neman kankane komai saboda jarin hujja, ba za su so hakan ba, amma kuma al’ummun duniya mafiya rinjaye sun san taimakon juna da yin hadin gwiwa su ne maganin kalubalen da ake fuskanta ba ma a bangaren fasahohin zamani ba, har da rashin tabbas da duniya ke kaka-ni-ka-yi a ciki.

Idan aka biye wa masu son a boye ko a zabi wadanda za su ci gajiyar fasahohin zamani ta hanyar da aka ga dama, fargabar da ake da ita ta fuskar amfani da su wajen aikata barna za ta ci gaba da karuwa har ta kai ga illata duk wasu muhimman sassa na rayuwa, domin a boye babu wanda zai san abubuwan da ake aikatawa.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Kasar Sin ta jaddada muhimmancin karfafa ilmantarwa kan hadurran fasahohin, da tabbatar da cewa komai na sha’anin AI ya kasance a hannun dan Adam, da karfafa tafiya da kowa da kowa wajen tsara ka’idoji da kuma raba cin gajiya ta yadda za a cike gibin da ke tsakanin hamshakan kasashe da masu tasowa.

Kafuwar WAICO ta kasance tamkar kaya ya tsinke a tushen kaba, domin ta zo a lokacin da ake tsananin bukata saboda karuwar fargabar duniya game da makomar fasahar AI. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

AI
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace
  • Sulaiman
    Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
  • Sulaiman
    Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum
AI
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

MASU ALAKA

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya
Daga Birnin Sin

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya
Daga Birnin Sin

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Next Post
Akpabio

Tinubu Ya Dukufa Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro — Akpabio

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.