Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ƙara ƙaimi wajen magance matsalar rashin tsaro, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba matsalar za ta zama tarihi.
Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin Ƙungiyar “Ladies Golf Association of Nigeria”, ƙarƙashin jagorancin shugabarta ta ƙasa, Dakta Lima Ahmed, a wata ziyarar girmamawa da suka kai Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ke Abuja.
Bayanin na Akpabio na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Jackson Udom, ya fitar.
Gwamnatin Tarayya ta sha yin alƙawarin dawo da tsaro a ƙasar ta hanyar ƙara ƙarfin ayyukan sojoji da sauran matakan da ta ke ɗauka.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Akpabio ya ce nasarar ceto ɗaliban makaranta da aka sace a Jihar Oyo a baya-bayan nan ta nuna ƙudurin gwamnatin tarayya na magance matsalar rashin tsaro a faɗin ƙasar.













