ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Inganta Makarantu: Gwamna Lawal Ya Sanya Hannu Kan Dokokin Gyaran Ilimi A Zamfara

by Sulaiman
2 months ago
Makarantu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanya hannu kan wasu Dokokin Zartarwa da za su kafa sabon tsarin gudanar da harkokin ilimi a jihar, tare da ƙaddamar da rabon Manhajar Karatu ta Ƙasa ga makarantun gwamnati.

Gwamnan ya ƙaddamar da shirin ne a ranar Talata yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau.A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa dokokin zartarwar sun ƙunshi sabbin tsare-tsaren gudanar da harkokin kuɗaɗen ilimi, kare makarantu, tantance nau’o’in makarantu, tabbatar da ingancin ilimi, kula da lafiyar ɗalibai da kuma inganta tsaro a makarantu.

Makarantu

Sanarwar ta ce, gyare-gyaren sun kuma shafi yadda za a gudanar da makarantu, tsarin ciyar da ɗalibai, walwalar ɗalibai, tabbatar da tsaron zirga-zirgar makaranta, aiwatar da shirin Makarantu Masu Tsaro (Safe Schools Initiative) da kuma tsara yadda ake gudanar da bukukuwan kammala karatu.Bugu da ƙari, gwamnatin ta kuma gabatar da sauye-sauye da suka haɗa da gudanar da jarrabawa a tsari guda, inganta ayyukan kula da lafiyar makarantu, naɗin shugabannin makarantu bisa cancanta, bunƙasa ilimin bai ɗaya, da kuma ƙarfafa koyar da Kimiyya, Fasaha, Injiniyanci da Lissafi (STEM), Ilimin Fasaha da Sana’o’i (TVET) da ilimin zamani na fasahar dijital.Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa ilimi ya fi kasancewa kawai wata hidimar zamantakewa.

ADVERTISEMENT

Ya ce ilimi shi ne mafi ƙarfi wajen rage talauci, samar da zaman lafiya, ƙarfafa tsaro, haɓaka tattalin arziki da kuma shirya matasa domin fuskantar ƙalubalen duniya mai dogaro da ilimi.“A yau muna mayar da wannan ƙuduri zuwa matakan da za su ɗore ta hanyar sanya hannu da kuma ƙaddamar da waɗannan Dokokin Zartarwa.“Waɗannan dokoki ba umarni ne daban-daban ba. Tsarin mulki ne cikakke da aka tsara domin inganta tafiyar da makarantu, ƙarfafa riƙon amana, kare kadarorin ilimi na gwamnati, inganta yadda ake samar da kuɗaɗen ilimi, tabbatar da tsaro, ɗaga darajar ilimi, inganta sakamakon karatu da kuma shirya yaranmu domin ƙarni na 21,” in ji gwamnan.

Ya ƙara da cewa, tsawon shekaru an fi mayar da hankali wajen gina azuzuwa da dakunan gwaje-gwaje, amma ƙwarewa ta nuna cewa gine-gine kaɗai ba su wadatar wajen samar da ingantaccen ilimi.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Makarantu

Tun da farko, Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar Zamfara, Abdulmalik Abubakar Gajam, ya ce nasarar kowace manhajar gyaran ilimi na dogara ne da haɗin gwiwar gwamnati, malamai, iyaye, al’umma, sarakunan gargajiya, abokan hulɗar ci gaba da kuma masu zaman kansu.

Ya bayyana cewa manufar waɗannan gyare-gyare ita ce tabbatar da makarantu masu tsaro, ingantaccen shugabanci, lafiyar ɗalibai, kyakkyawan koyarwa, sakamako mai inganci a fannin ilimi da kuma ƙara yawan amincewar jama’a da tsarin ilimin jihar.

Makarantu
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Taron AI Na Duniya: Kaya Ya Kwance A Tushen Kaba

Taron AI Na Duniya: Kaya Ya Kwance A Tushen Kaba

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.