Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna albarkacin cika shekaru 55 da kulluwar diplomasiyya tsakanin kasar Sin da Amurka daga wasan Kwallon Tebur watau Ping-Pong Diplomacy a yau Juma’a.
Shugaba Xi Jinping ya nanata cewa, jama’a ne suka gina tushen dangantakar Sin da Amurka, kana matasa ne suka kirkiro makomarta. Ya ce fatan ita ce, jama’a daga kowane bangare na rayuwa a kasashen biyu, musamman matasa, za su dauki darasi na hikima da karfi daga tarihi, da zurfafa fahimtar juna da abota ta hanyar musaya da hadin gwiwa, da samun ci gaba kafada da kafada ta hanyar koyi da juna da hada hannu wajen karfafa abota da bayar da sabbin gudunmuwa ga inganta dangantakar Sin da Amurka cikin aminci da karko da dorewa.
A watan Afrilun 1971 ne wata tawagar ‘yan wasan kwallon Tebur na Amurka ta kawo ziyara kasar Sin, inda ta zama tawaga ta farko ta Amurkawa da ta ziyarci Sin cikin gomman shekaru. Wannan ziyara, ita ce mafarin abun da ake kira da Ping-Pong Diplomacy, haka kuma ta taimaka wajen share fagen kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka.(Fa’iza Mustapha)














Discussion about this post