A kwanan nan shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasikar da wasu matasan dalibai ‘yan kasar Australia su 110 suka rubuta masa, inda a cikin wasikar tasa ya karfafa gwiwarsu da su himmatu wajen yaukaka kawancen Sin da Australia.
Cikin wasikar ta shugaba Xi, wadda ya aike ga daliban a ranar 28 ga watan Oktoba da ya shude, ya ce ya yi farin cikin jin cewa a baya bayan nan daliban sun ziyarci kasar Sin domin halartar gasar tseren kwale-kwale da gasar Dragon Boat, inda suka fafata tare da takwarorinsu na jami’o’in kasar Sin, kana sun zurfafa musaya, da kulla abota wadda ta zarce kan iyakokin kasashensu, tare da nishadantuwa cikin lokaci mai kayatarwa.
Daga nan sai shugaban na Sin ya bayyana fatan cewa daliban na Australia, za su ci gaba da bayar da gudunmawa a fannin ingiza kawance tsakanin kasashen biyu, tare da zama jakadun abota, da hadin gwiwar sassan biyu, kana za su ingiza wannan abota daga zuri’a zuwa zuri’a.
A ‘yan kwanakin baya ne daliban na kasar Australia daga jami’ar Sydney da wasu karin jami’o’in, suka yi hadin gwiwar rubuta wasika ga shugaba Xi, da firaministan Australia Anthony Albanese, suna masu bayyana abubuwan da suka faru yayin ziyararsu a kasar Sin. (Saminu Alhassan)













