Yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta’aziyya ga shugaban Nepal Ram Chandra Poudel, game da ibtila’in zabtarewar laka da ya faru a Nepal.
Xi Jinping ya bayyana cewa, mummunan ibtila’in da ya faru a Gyirong-Rasuwa dake iyakar kasar Sin da Nepal kwanan nan, ya haifar da asarar rayuka da bacewar mutane, da kuma asarar dukiya masu yawa. Kuma a madadin gwamnati da al’ummar Sin, yana juyayin asarar rayukan da ibtila’in ya haifar, sannan ya isar da sakon jaje ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da wadanda suka jikkata, da kuma mutanen da ke yankunan da ibtila’in ya shafa.
Bisa labaran da wakilan babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG suka ruwaito, ibtila’in ya haifar da asarar rayuka da bacewar mutane masu yawa a bangaren Sin. Ya zuwa karfe 3:00 na yammacin yau Jumma’a, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar, sannan mutane 558 sun bace a Sin.
A wani labarin a yau din, kafin ziyarar aikinsa a kasar Kyrgyzstan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya wallafa wata makala mai taken “Hada Kai Don Bude Sabon Babi na Ci Gaba Mai Inganci a Huldar Sin da Kyrgyzstan” a wasu kafafen watsa labarai na Kyrgyzstan.(Safiyah Ma)














