Masana’antar sarrafa bayanai ta kasar Sin ta ci gaba da fadada cikin sauri a shekarar 2025, inda take tallafa wa raya bangaren fasahar kirkirarriyar basira ta AI da ke samun ci gaba cikin sauri.
Alkaluman da aka fitar yayin bude baje kolin masana’antar manyan bayanai ta Big Data ta kasa da kasa ta kasar Sin a yau Juma’a sun nuna cewa, darajar masana’antar a shekarar 2025 ta kai yuan triliyan 6.78, kwatankwacin dala triliyan 1, adadin da ya karu da kaso 15.7 kan mizanin shekara shekara.
Jimilar darajar da baki dayan kayayyakin sarrafa bayanai da suka shafi manhajoji, ciki har da manhajar AI, da albarkatun bayanai, ciki har da hidimomin samar da bayanai suka samar, ta kai yuan triliyan 4.99, wadda ta dauki kaso 73.6 na jimilar masana’antar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)













