Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin umarni, wanda a cikinsa ya bukaci a kara azamar dakile aukuwar muggan hadurra, bayan da gobara ta tashi a cikin wani jirgin ruwan dakon kayayyaki a birnin Qingdao na lardin Shandong dake gabashin kasar.
Shugaba Xi, ya jaddada bukatar gaggauta aiwatar da bincike da ceton rayukan wadanda suka bace, tare da hanzarta shawo kan ibtila’in, da samar da natsuwa ga iyalan wadanda lamarin ya shafa, kana da gaggauta gano musabbabin aukuwar lamarin. A lokaci guda kuma, a aiwatar da hukuncin shari’a, da tsauraran matakai kan duk wanda aka samu da hannu cikin aukuwar lamarin.
Rahotanni na cewa mutane 25 sun rasu, sakamakon gobarar da ta tashi a wani jirgin ruwan dakon kaya na ketare a birnin Qingdao na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin.
Hukumar kashe gobara da ayyukan ceto na Qingdao, ta ce jirgin ruwan ya kama wuta ne da karfe 11 da mintuna 15 na tsakar ranar yau, yayin da ake gyaransa a wani wurin turke jiragen ruwa mallakin wani kamfanin kirar jiragen ruwa na Sin.
Hukumar ta ce jirgin na dauke da jimillar mutane 42. An kuma yi nasarar tseratar da mutum 12 lami lafiya, kana an garzaya da mutum biyar da suka jikkata zuwa asibiti, kuma ba sa cikin wani babban hadari.
Yanzu haka dai an aike da jami’an hukumar ayyukan gaggawa, da na kashe gobara da ayyukan ceto, da ‘yan sanda, da sassan kula da lafiya zuwa wurin da lamarin ya faru domin bincike da aikin ceto. (Saminu Alhassan)














