Rahotanni daga kungiyar sa kaimi ga cinikayya ta kasar Sin, za a gudanar da taron koli na shugabannin harkokin masana’antu, da cinikayya na kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta nahiyar Asiya da tekun Pasifik wato APEC, na shekarar 2026 a ranakun 17 da 18 ga watan Nuwamban bana a birnin Shenzhen dake kasar Sin.
Kakakin kungiyar ya yi bayanin cewa, taken taron shi ne “Sa kaimi ga samun wadata da kyakkyawar makoma tare”, kuma kungiyar za ta karbi bakuncin gudanar da taron, inda za a gayyaci wakilai daga bangarorin siyasa, da cinikayya na kasashe da yankunan membobin APEC kimanin su 1000 zuwa taron.
Ana sa ran yin musayar ra’ayoyi game da raya yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Asiya da tekun Pasifik, da yin mu’amala, da hadin gwiwa da juna, da raya fasahar AI, da tattalin arziki ta dijital, da raya yankin Guangdong-Hong Kong-Macau na kasar Sin, da samun ci gaba mai dorewa da sauransu, don ba da shawarwarin sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin nahiyar Asiya da tekun Pasifik baki daya. (Zainab Zhang)














