A yau Lahadi, shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya gabatar da shawarwari guda biyar game da hadin gwiwar “gawurtacciyar kungiyar BRICS” a fannonin fasahar kirkirarriyar basira ta AI, da saukaka harkokin kasuwanci da zuba jari, da masana’antar samar da fasahar zamani, watau digital, da kamfanoni masu aiki da fasahar zamani, da kuma bunkasa samar da hazikai.
Xi ya gabatar da wadannan shawarwari ne yayin da yake halartar taron kolin BRICS a rana ta biyu a birnin New Delhi.
Xi ya jaddada cewa, ya zama wajibi “gawurtacciyar kungiyar BRICS” ta samar da manyan alfanu, da cimma gagarumin ci gaba, tare da shimfida harsashi mai kwari domin gudanar da hadin gwiwa a aikace.
Xi ya bayyana cewa, ya kamata “gawurtacciyar kungiyar BRICS” ta yi amfani da karfinta na kasancewa tushe a fagen kasuwanni masu tasowa da kuma hadewa da kasashe masu tasowa a duniya, tare da tabbatar da riko da manufar bude kofa da hadin gwiwa domin samun moriyar juna da nasara ga kowane bangare, da kiyaye tsarin masana’antu da na samar da kayayyaki ba tare da tangarda ba, kana da karfafa hadewar kasuwanni da juna.
Ya kuma yi nuni da cewa, ya kamata “gawurtacciyar kungiyar BRICS” ta gina wuraren kyankyasar sabbin kirkire-kirkire, da daga darajar tsoffin masana’antu, da habaka masana’antu masu tasowa, sannan ta yi wasu tsare-tsare na hangen nesa ga masana’antu na gaba, ta yadda sabbin fasahohin zamani za su iya haskaka hanyar samun wadata ta bai-daya.
Bugu da kari, yayin da yake nuni da cewa a wannan shekara ce aka fara aiwatar da shirin bunkasa ci gaban kasa da kyautata zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar na kasar Sin karo na 15, Xi ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa samun ci gaba mai inganci a matakin koli, da fadada bude kofa mai matukar inganci, da aiwatar da shawarar bunkasa ci gaban duniya, da zurfafa hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya a matakin koli, tare da rarraba damammaki da kuma bude hanyoyin samun wadata tare da sauran kasashe a sassan duniya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)













