ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, September 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

by Sulaiman and Muh'd Shafi'u Saleh
51 minutes ago

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

Fitattun ’yan Nijeriya, ciki har da attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri da tsohon Gwamna Umar Jibrilla Bindow, sun halarci jana’izar tsohon gwamnan tsohuwar Jihar Gongola kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Alhaji Bamanga Muhammad Tukur, a Yola.

An gudanar da sallar jana’izar marigayin ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe ranar Lahadi, 13 ga Satumba, 2026, a Masallacin Fadar Lamidon Adamawa da ke Yola, kafin daga bisani aka binne gawarsa a gidansa bisa tsarin koyarwar Musulunci.

Gwamna Fintiri ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar, wadda ta haɗa da mambobin Majalisar Zartarwa, ’yan Majalisar Dokoki ta Jiha da ta Ƙasa, da manyan jiga-jigan PDP.

Haka kuma, jana’izar ta samu halartar ɗimbin sarakunan gargajiya da masu riƙe da sarautu, ƙarƙashin jagorancin Lamidon Adamawa, Mai Martaba Dr. Barkindo Aliyu Musdafa. Daga cikin waɗanda suka halarta akwai Sarkin Fofure, Ganwarin Masarautar Ganye da Ptil Madagali, tare da hakimai da sauran shugabannin al’umma daga ƙananan hukumomi 21 na jihar.

Alhaji Aliko Dangote ma yana cikin manyan waɗanda suka halarci jana’izar, tare da tsofaffin ministoci, sanatoci, ’yan kasuwa da manyan malaman addinin Musulunci.

Da yake bayyana rasuwar Tukur a matsayin babban rashi ga jihar da ƙasa, Gwamna Fintiri ya ce marigayin ya kasance uba, jagora kuma mai ba da shawara ga mutane da dama.

Fintiri ya ce, “Mun koyi abubuwa da dama daga gare shi. Rasuwarsa ta bar babban gibi wanda Allah kaɗai zai iya cikawa. Za mu ci gaba da yi masa addu’ar Allah Ya sa Aljanna ce makomarsa.”

Shi ma Dangote ya bayyana rasuwar Tukur a matsayin babban rashi ga Nijeriya, musamman ga ’yan kasuwa, tare da addu’ar Allah Ya yi masa rahama.

Bamanga Tukur ya rasu ne ranar Asabar a Abuja, kwanaki uku kacal kafin cika shekaru 91 da haihuwa.

Ya bar mata biyu da ’ya’ya 18, ciki har da Sakataren Gwamnatin Jihar Adamawa, Auwal D. Tukur.

Marigayin ya kasance fitaccen ɗan siyasa kuma dattijo mai kishin ƙasa, wanda ya taɓa zama Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola, sannan ya taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasa da gudanar da ayyukan gwamnati a Nijeriya.

Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU
  • Sulaiman
    Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”
  • Sulaiman
    Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya
  • Sulaiman
    Doma United Na Cigaba Da Jan Zarenta A Firimiyar Nijeriya Bayan Doke Enyimba
Muh'd Shafi'u Saleh
+ posts Bio
  • Muh'd Shafi'u Saleh
    https://hausa.leadership.ng/author/muhd-shafiu-saleh/
    Jami’in Tsaro Ya Mayar da Dala 505 Da Riyal 30 Da Ya Tsinta A Yola
  • Muh'd Shafi'u Saleh
    https://hausa.leadership.ng/author/muhd-shafiu-saleh/
    Shahararren Malamin Addinin Islama A Adamawa Sheikh Ibrahim Abubakar Daware Ya Rasu
  • Muh'd Shafi'u Saleh
    https://hausa.leadership.ng/author/muhd-shafiu-saleh/
    An Yi Wa ‘Yansanda 110 Ƙarin Girma A Adamawa
  • Muh'd Shafi'u Saleh
    https://hausa.leadership.ng/author/muhd-shafiu-saleh/
    Gwamna Fintiri Ya Nada Sabbin Sarakuna 7 A Jihar Adamawa
ADVERTISEMENT

MASU ALAKA

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya
Manyan Labarai

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

September 13, 2026
Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa
Manyan Labarai

Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

September 13, 2026
Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91
Manyan Labarai

Tsohon Shugaban PDP Na Ƙasa Bamanga Tukur Ya Rasu Yana Da Shekara 91

September 12, 2026
Next Post
Yajin Aikin ASUU: Malaman Jami’ar Jihar Kaduna Sun Bijirewa El-rufa’i

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU

LABARAI MASU NASABA

Yajin Aikin ASUU: Malaman Jami’ar Jihar Kaduna Sun Bijirewa El-rufa’i

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU

September 13, 2026
Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

September 13, 2026
Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”

Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”

September 13, 2026
Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

September 13, 2026
Doma United Na Cigaba Da Jan Zarenta A Firimiyar Nijeriya Bayan Doke Enyimba

Doma United Na Cigaba Da Jan Zarenta A Firimiyar Nijeriya Bayan Doke Enyimba

September 13, 2026
Hafsat Bakari Ta Sake Dawo Da Sarƙaƙƙen Al’amari

Hafsat Bakari Ta Sake Dawo Da Sarƙaƙƙen Al’amari

September 13, 2026
Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

September 13, 2026
Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

September 12, 2026
Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

September 12, 2026
jam'iyyu

An Buƙaci Ƴan Takara Su Sanya Tsare-tsaren Yaƙi Da Ɗumamar Yanayi A Jaddawalin Kamfen Ɗinsu

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.