ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matatar Man Dangote Ta Dawo Sayar Da Fetur A Dala

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
Dangote

Matatar Man Dangote ta sauya tsarin biyan kudin sayen Man Fetur (PMS), Dizal (AGO) da Man Jirgin Sama (ATK) zuwa Dalar Amurka.

Sabon tsarin, wanda ya fara aiki nan take, ya shafi sayar da man fetur kai tsaye daga matatar (gantry) da kuma sayar da shi ta hanyar jigilar ruwa.

Majiyoyi daga masana’antar da ke da masaniya kan ayyukan matatar sun bayyana cewa an dauki wannan mataki ne sakamakon karuwa da hadarin sauyin canjin kudaden waje, wanda ya samo asali daga tsarin sayen danyen mai da matatar ke amfani da shi da kuma ci gaba da rashin daidaito a kasuwar musayar kudaden waje.

ADVERTISEMENT

A cewar wani babban jami’i a masana’antar, yanzu matatar na karbar mafi yawan danyen man da take tacewa daga Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) ne bisa yarjejeniyar da ake biyan kudinta da Dalar Amurka, yayin da babban kaso na kayayyakin man da take tacewa ake ci gaba da sayar da su cikin Naira.

Majiyar ta bayyana cewa wannan rashin daidaito tsakanin sayen danyen mai da Dala da kuma sayar da kayayyakin da Naira ya jefa matatar cikin babban hadarin canjin kudi, wanda ya sa ta ga ya zama dole ta koma tsarin sayar da kayayyakinta da Dala.

LABARAI MASU NASABA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

“Wannan mataki ya fara aiki nan take. Dukkan tallace-tallacen PMS, AGO da ATK, ko ta hanyar gantry ko ta teku, yanzu za su kasance da Dalar Amurka,” in ji majiyar.

An kuma bayyana cewa an aika da takardar sanarwa ga dillalan da ke daukar man fetur daga matatar domin sanar da su wannan sabon tsari.

Wani jami’in ya kara da cewa ci gaba da sauye-sauyen farashin danyen mai a kasuwannin duniya da kuma rashin tabbas a kasuwar musayar kudaden waje ta Nijeriya su ma sun taka rawa wajen yanke wannan shawara.

A cewarsa, yanzu matatar na samun kananan jigilar danyen mai da ake saye da Naira idan aka kwatanta da wadanda ake saya da Dala, alhali kuma mafi yawan kayayyakin man da take tacewa ana sayar da su a kasuwar cikin gida da Naira.

“Muna bukatar sama da jigilar danyen mai 15 a kowane wata domin gudanar da ayyukanmu, amma NNPCL na fama da samar da ko da jigila uku da ake biya da Naira karkashin tsarin musayar Naira da danyen mai,” in ji wani jami’in.

Masana harkokin kasuwa sun yi hasashen cewa wannan sabon tsari na iya yin tasiri sosai kan farashin man fetur, kudin rarrabawa da kuma bukatar Dalar Amurka, musamman ganin cewa Matatar Dangote na daya daga cikin manyan masu samar da tataccen man fetur a Nijeriya.

Da yake tsokaci kan lamarin a wata hira da Daily Trust, wani masanin harkokin mai da iskar gas, Otunba Tunji Oyebanji, cewa ya yi:

“Hakan na nufin ko dai ba ya samun isasshen danyen mai, ko kuma tsarin da aka tsara bai yi aiki yadda aka zata ba. Tun farko mun ce wannan babban kalubale ne. Nijeriya ba ta samar da isasshen danyen mai tun da farko. Sannan an riga an yi alkawarin wani kaso na danyen man ga wasu kamfanoni. An karbi kudi a gaba daga wasu masu saye, kuma yanzu ana biyansu da danyen mai. Wannan ya rage adadin danyen man da za a iya sayar wa Dangote ko kuma a kasuwannin duniya.”

Ya ci gaba da cewa: “Kar a manta cewa danyen mai shi ne babban abin da Nijeriya ke samun kudaden shiga daga fitarwa. Ba wai ina kare NNPCL ba ne, amma wannan na iya kasancewa daya daga cikin matsalolin da suka sa tsarin bai yi nasara ba.”

Oyebanji ya kara da cewa: “Abin da hakan ke nufi shi ne Dangote zai rika sayen karin danyen mai daga kasashen waje, kuma dole ne ya biya da Dala. Ina ganin wannan ne ya sa ya yanke shawarar fara sayar da kayayyakinsa da Dala. Tasirin hakan kuwa shi ne zai kara bukatar Dalar Amurka a kasuwa, wanda hakan na iya kara raunana darajar Naira.”

Dangote
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Next Post
Gasar Kofin Duniya: Da Ƙarfinmu Muka Kawo Matakin Da Muke Yanzu – Messi

Gasar Kofin Duniya: Da Ƙarfinmu Muka Kawo Matakin Da Muke Yanzu – Messi

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.