Rundunar ’yansandan Jihar Zamfara ta ce ta kashe ’yan bindiga sama da 30 da ake zargi da kai hari a garin Bukkuyum da ke Ƙaramar Hukumar Bukkuyum ta jihar.
Lamarin ya faru ne a ranar 28 ga watan Oktoba, 2026, lokacin da ’yan bindigar suka yi ƙoƙarin shiga garin.
Sai dai jami’an ’yansanda tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron sa-kai sun yi musayar wuta da su tare da hana su shiga garin.
Mai magana da yawun rundunar ’yansandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya ce daga baya an gano gawarwaki sama da 30 da ake zargin na ’yan bindigar ne a gonakin da ke kewaye da garin.
Ya bayyana cewa jami’an tsaron sun hana aukuwar asarar rayuka, lalata dukiyoyi da kuma tilasta wa jama’a barin gidajensu.
Rundunar ’yansandan ta ce za ta ci gaba da gudanar da samame tare da sauran hukumomin tsaro domin kawar da ’yan bindiga da tabbatar da zaman lafiya a yankin.














