Shugaban kasar Sin, Xi Jinping zai je ziyarar aiki a Amurka daga ranar 23 zuwa 25 ga watan Satumba bisa gayyatar shugaban Amurka, Donald Trump, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun, ya sanar a yau Litinin.
A yayin ziyarar dai, Xi da Trump za su yi musayar ra’ayoyi mai zurfi kan manyan batutuwan da suka shafi dangantakar Sin da Amurka da kuma zaman lafiya da ci gaban duniya, in ji mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ta Sin a wani taron manema labarai na yau da kullum.
Kazalika, Guo ya ce diflomasiyyar shugabannin kasashen tana taka rawar ganin da ba za a iya maye gurbinta ba wajen samar da jagoranci bisa manyan tsare-tsare ga dangantakar Sin da Amurka, kuma ziyartar juna ta shugabannin kasashen biyu a cikin watanni shida na nuna wani muhimmin ci gaba mai tarihi.
Ya kuma kara da cewa, Sin a shirye take ta yi aiki tare da bangaren Amurka wajen fadada dangantaka mai ma’ana bisa manyan tsare-tsare cikin kwanciyar hankali, da karfafa tattaunawa da hadin gwiwa, da warware sabani yadda ya kamata, da kuma ci gaba da ba da gudummawa ga kyautata jin dadin al’ummomi da zaman lafiyar duniya, da kwanciyar hankali da kuma samun wadata. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














