ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Al’umma Suka Gudanar Da Bukukuwan Sallah Duk Da Matsin Tattalin Arziki

by Rabi'at Sidi Bala
5 days ago
Al'umma

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zaƙulo muku batutuwa daban-daban waɗanda suka shafi al’umna.

Tsokacinmu na yau zai yi duba game da abin da ya shafi tsadar rayuwa musamman a wannan sallah da ta gabata.

Inda shafin ya ji ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; “Ya tsadar abun layya ya kasance a wurarenku, ko jama’a sun samu damar yin layya fiye da yadda ake tunani?, Wanne irin bambanci aka gani game da sallar Bara da ta Bana, musamman wajen yin abun layya da kuma shagulgulan sallah?, ko wacce shawara za a bawa al’umma game da ci gaban rayuwarsu musamman waɗanda basu samu damar yin layya ba, da kuma waɗanda suke takurawa kansu gudun kada ace ba su da shi?”.

ADVERTISEMENT

Ga dai bayanan nasu kamar haka:

Sunana Aminu Adamu, Malam Madori daga Jihar Jigawa:

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za Ku Tattala Kuɗaɗen Da Ke Shigowa Hannu Domin Ci Gaban Rayuwa

Aure Ba Sana’a:Imani Ko Ganganci?

To, magana ta gaskiya abun layya yayi tsada sosai, saboda tsadar abubuwan kiwo kama daga dusa zuwa harawar gyaɗa, wannan dalili ne ya sa abun layya yake nema ya gagari mai ƙaramin ƙarfi. Haƙiƙa akwai bambanci sosai tsakanin sallar bana da ta bara, domin bara dabbobi ba suyi tsada irin ta wannan shekarar ba, sai kuma bana akwai sauƙin abinci ba kamar bara ba. Shawarata a nan ita ce duk waɗanda Allah ya ba su damar yin layya ya kamata su godewa Allah kuma su taimakawa masu ƙaramin ƙarfi na kusa da na nesa, su ma su wadata da nama a irin wannan lokaci na babbar sallah.

Sunana Sarauniya Nasmah, daga Jihar Zamfara:

Tsadar abin layya a Jihar zamfara a wannan karon ya ƙaru, duk da ba Jihar mu kawai ake fuskantar wannan matsalar ba, wannan matsala ce gama-gari, wannan dalilin ya sa mutane da dama abu ne mai wahala su yi layya. Bambancin sallar bara da ta bana kuwa a bayyane yake; bambancin kuɗi, waccan tafi wannan, ko wajen ɗinka suturu duk da dama sallar nama ba kasafai ake ɗinke-ɗinke ba. Shawarata ga al’umma kuwa shi ne ka dage da addu’a , tsanani yana tare  da sauƙi, matsin rayuwa da muke ciki dole sai an haɗa da addua kuma mun tashi tsaye domin neman mafita.

Sunana Lawan Ismail (Lisary), Rano daga Jihar Kano

Gaskiya kafin watan sallah ya kama suna tsada amma yanzu basa yi, duba da ƙarancin kuɗi a hannun al’umma. Bana layya ba sosai ba aka yi ba gaskiya. Bana ba kamar bara ba, saboda rashin kuɗi, gashi bana lokacin ya zo daidai da faɗuwar damuna. Shawarata a nan ita ce mutane kada su takurawa kansu idan babu halin yin layya duba da matsin rayuwar da muke ciki a yanzu.

Sunana Princess Fatima Mazadu, daga Jihar Gombe:

Maganar gaskiya ta Allah ce, yin laiya ga al’umma duk da wajibcinta, amma gaskiya tsadar dabobi ya yi yawa sosai a sassan ƙasar nan, musamman da ta zo mana a damuna kaya dama irin wannan sun fi tsada saboda lafiyar yanayin. Bambancin ƙarancin kam! babu, saboda bana ma tsada suke bara ma haka, sai dai wataƙila daga baya mu ji sun sauko tunda ba yadda Allah ba ya yi.

Shagulgula sai abun da ya ƙaru musamman garina Gombe da aka ƙara ƙawata hawa na al’adu da sabbin sarautu. Su kwantar da hankalinsu, niyya ta isar wa mai duka, Allah ne mai bada ikon, kuma idan bai bayar ba sai a gode masa a cigaba da harkoki tunda akwai babban wato lafiya.

Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato:

A bana dai gaskiya ba kamar bara ba, jama’a da dama ba su samu damar yin layya ba, saboda tsadar abin yanka. Dabbobin layya sun yi tsada, kuɗi kuma ya yi wahala, saboda tsadar rayuwa. Sai dai Alhamdulillahi, an samu an yi hidimar sallah cikin rufin asiri da kwanciyar hankali.

Waɗanda suka samu damar yin layya daga ƴan’uwa da maƙwafta, sun raba nama da waɗanda ba su samu sun yi ba. Wannan dama wata tsohuwar al’ada ce ta Bahaushe a duk lokaci irin wannan. Da fatan Allah Ya karɓi ayyukanmu na ibada, Ya ƙara buɗa mana al’amuranmu.

Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano:

Alhmadulillah! Za mu ce, amma bana dai abin yanka yana wuta, dan ma dai Allah shi ne mai komai a haka dai ake siya. Ga dukkan alamu bana ba kamar Bara ba, duba da cewa an saba da tsadar abin yanka ana ta hada-hada a gari na ta shirin sallah ko ina an fara ɗaukar harami! Bara dai an fi jin gari. Idan Allah Bai baka ikon yi ba to ka haƙura kawai Allah ya Kaimu gaba, kar a zo ciyo bashi, ƙarshe a zo ana kaka naka yi.

Sunana Sadik Abubakar Abdullahi, Rijiyar Lemo, Karamar Hukumar Dala, a Jihar Kano:

A bana an samu tsadar dabbobin layya da sauran kayayyakin bukukuwan sallah sun ƙaru sosai idan aka kwatanta da shekarun baya, wannan ya sa mutane da dama suka shiga tunani kafin su yanke shawarar yin layya. A wasu garuruwa akwai waɗanda suka samu damar yin layya duk da halin matsin rayuwa, amma ba kamar yadda aka saba gani a baya ba, domin mutane da yawa sun rage kashe kuɗi tare da neman dabbobi masu sauƙin farashi.

Duk da haka, an samu masu ƙoƙarin cika sunnah gwargwadon hali, yayin da wasu suka fi mayar da hankali kan gudanar da ibada cikin natsuwa ba tare da takura wa kansu ba. Idan aka kwatanta da bara, a bana an fi nuna taka-tsantsan wajen shagulgula da kashe kuɗi saboda yanayin tattalin arziki.

Mutane da yawa sun fahimci cewa muhimmancin salla ba wai yawan hidima ko nuna hali ba ne, illa ibada, zumunci da taimakon juna. Shawarar da ya kamata a bai wa al’umma ita ce su guji shiga wahala ko cin bashi domin neman suna a lokacin salla. Layya ibada ce ga mai hali, kuma wanda bai samu dama ba bai kamata ya ji ƙasƙanci ko damuwa ba. Haka kuma masu hali su riƙa taimaka wa marasa ƙarfi domin a samu farinciki da haɗin kai a tsakanin al’umma.

Sunana Hafsat Sa’eed, daga Jihar Neja:

A gaskiya dai yin layya a yanzu mussamman a nan Neja yayi matuƙar wuya duba da tsadar dabbobi ya hau,  amma Alhamdulillah har yanzu da yawa suna yin layya, Allah ya na cigaba da hore wa  Al’umma musulmi. Idan aka kwatanta sallar bana da ta bara, farashi ya yi yawa kuma ana yanka dabbobi kaɗan, wasu ma basu samu halin yin layyar ba, tare da ƙarancin kashe kuɗi.

Shawarata ita ce, wanda Allah Ubangiji ya horewa, ya mayar hankali kan sadaka musamman wajen yin layya da tallafawa al’umma, musamman mu a nan Neja Alhamdulillah, al’umma sun yi iyakar ƙoƙarinsu wajen ganin sun sadakar da naman layyarsu ga al’umma mabuƙata. Kuma a cigaba da aikata alheri da haƙuri.

Sunana Anas Bin Malik, Achilafiya Ƴankwashi, a Jihar Jigawa:

A wannan shekarar, tsadar abin layya ta yi yawa sosai saboda matsin tattalin arziƙi da hauhawar farashi, lamarin da ya sa mutane da dama suka kasa yin layya kamar yadda suka saba.

Duk da haka, wasu sun yi iya ƙoƙarinsu domin gudanar da ibadar, saboda muhimmancinta a addini. Idan aka kwatanta sallar bara da ta bana, an ga cewa shagulgula sun ragu, mutane kuma sun fi gudanar da sallah cikin sauƙi da takaitawa.

Mutane su fi karkata ga taimakon juna da kula da iyali maimakon nuna isa ko kwaikwayon rayuwa. Ya kamata a tunatar da al’umma cewa layya ibada ce da ake yi gwargwadon hali, don haka bai dace mutum ya takura kansa saboda tsoron abin da mutane za su ce ba.

Hakanan, masu hali su riƙa taimakawa marasa ƙarfi domin ƙarfafa zumunci da haɗin kai. Ana kuma buƙatar mutane su rungumi sana’o’i da hanyoyin neman na kai domin inganta rayuwarsu da rage wahala.

Sunana Sama’ila Muhammad

Tabbas akwai tsada amma ba kamar bara ba, bana ga ragunan  amma babu masu siya hakan ya:sa suka ɗan yi sauƙi. Akwai bambanci sosai ga raguna a kasuwa burjik babu masu siya saboda rashin kuɗi a hannu. Bai zama dole sai ka yi ba sai idan kana da hali, haka addini ya ce don Allah za ka yi ba don mutane su gani ba.

Al'umma
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A 29-05-2027
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Za Ku Tattala Kuɗaɗen Da Ke Shigowa Hannu Domin Ci Gaban Rayuwa
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ya Kamata Mawaƙa Su Guji Munafunci Da Hassada Su Rungumi Juna —Fati UK

MASU ALAKA

Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Taskira

Yadda Za Ku Tattala Kuɗaɗen Da Ke Shigowa Hannu Domin Ci Gaban Rayuwa

May 24, 2026
Al'umma
Taskira

Aure Ba Sana’a:Imani Ko Ganganci?

May 16, 2026
Bukatar Hada Hannun Iyaye Wajen Tarbiyar ‘Ya’yansu
Taskira

Bukatar Hada Hannun Iyaye Wajen Tarbiyar ‘Ya’yansu

May 2, 2026
Next Post
Nagartattun Manufofin Sin Suna Janyo Hankalin Kasashen Duniya

Nagartattun Manufofin Sin Suna Janyo Hankalin Kasashen Duniya

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.