ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nagartattun Manufofin Sin Suna Janyo Hankalin Kasashen Duniya

by CGTN Hausa and Sulaiman
3 months ago
Children waves flowers and American and Chinese flags before President Donald Trump is greeted by Chinese President Xi Jinping at a welcome ceremony at the Great Hall of the People, Thursday, May 14, 2026, in Beijing. (AP Photo/Mark Schiefelbein)

A cikin watanni 6 da suka gabata, shugabannin kasashen da ke da kujerun dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da na kasashe mambobin kungiyar kasashe 7 masu karfin masana’antu ta G7, kusan dukkansu sun kawo ziyara kasar Sin daya bayan daya.

Dangane da batun, shahararren dan jarida na kasar Zimbabwe, Mabasa Sasa, ya rubuta wani bayani, wanda aka nuna shi a shafin yanar gizo na jaridar “The Herald” ta kasar Zimbabwe, inda ya ce, jami’ai da kafofin yada labarai na kasashen yamma su kan yi kokarin saka ra’ayin rashin amincewa da kasar Sin cikin zukatan mutanen Afirka, a yayin da su da kansu suke ta kokarin karfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin.

Mista Sasa ya ce, ya kamata kasashen Afirka su magance fadawa cikin tarkon tunani da aka haka musu, kuma su kara zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin.Sa’an nan, a nasa bangare, wani shehun malami dan Najeriya mai suna Olalekan Babatunde, a cikin makalarsa da aka buga a jaridar “The Nation” ta kasar Najeriya, ya ce babban dalilin da ya janyo shugabannin kasashe daban daban zuwa ziyara a kasar Sin, shi ne muhimmin matsayin da kasar Sin ke da shi a duniya, a fannonin tattalin arziki, da diflomasiyya, da kimiyya da fasaha, da tsare-tsaren raya kasa. Kana ya shawarci kasashen Afirka da su yi amfani da damammakin da kasar Sin ta samar, a kokarin raya tattalin arzikinsu.

ADVERTISEMENT

Hakika, akwai abubuwa da dama da suka janyo hankalin shugabannin kasashe daban daban don ziyartar kasar Sin, wadanda suka hada da matsayin kasar Sin mai muhimmanci a duniya, gami da wasu manyan manufofi na kasar.Da farko, tsarin tattalin arziki na gurguzu mai salon musamman na Sin ya tabbatar da yanayin ci gaban tattalin arzikin kasar cikin sauri.

Wannan tsari ya ba gwamnati damar samar da jagoranci mai karfi, da baiwa kamfanoni masu zaman kansu damar raya kansu bisa shirin raya kasa na dogon lokaci da gwamnati ta tsara. Saboda haka, a lokacin da bangarorin kasashe daban daban ke hulda da kasar Sin, suna hulda da wata babbar kasuwa, inda ake samun manufofi masu tabbaci, da makomar karuwa mai dorewa.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Na biyu shi ne, yadda kasar Sin ke tsayawa tsayin daka kan raya kasa ta hanyar lumana. A lokacin da kasar Sin ke hulda da sauran kasashe, ba ta son ganin taho-mu-gama da ake yi tsakanin rukunoni daban daban, wadanda suke da bambancin ra’ayi. Maimakon haka, kasar Sin na son karfafa cudanya da hadin gwiwa tsakanin mabambantan al’ummu, ta yadda za a iya tabbatar da moriyar dukkansu.

Kana na uku shi ne, ra’ayin kasar Sin na gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya.Bisa wannan ra’ayi ne, kasar Sin ta gabatar da shirin “Ziri Daya da Hanya Daya”, da shawarwari masu nasaba da harkokin raya kasa, da tsaro, da cudanyar al’adu, da kula da al’amuran duniya.

Ban da haka, kasar na son raba moriya tare da sauran kasashe, wanda ya zama dalilin da ya sa ta aiwatar da hadin gwiwa da kasashen dukkan nahiyoyin Asiya, da Turai, da Afirka, da Latin Amurka, bisa shirin “Ziri Daya da Hanya Daya”, da yafe wa kasashe 53 dake nahiyar Afirka da suka kulla huldar diflomasiyya da ita harajin fito, da dai sauransu.

A takaice dai, manufofin kasar Sin sun sa kasashe daban daban fahimtar cewa, hadin gwiwa tare da ita zai samar musu da kyakkyawar damar raya kai, da samun kwanciyar hankali, da zama masu walwala tare. (Bello Wang)

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Ƴan Majalisar Dokokin Ƙasa 54 Sun Rasa Tikitin Takara A Zaɓen Fidda Gwanin APC

Ƴan Majalisar Dokokin Ƙasa 54 Sun Rasa Tikitin Takara A Zaɓen Fidda Gwanin APC

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.