ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Rayukan Mutane Sama Da 86 Suka Salwanta A Kan Titin Nnamdi Azikiwe Da Ke Kaduna

by Alkazeem M. Shariff
4 months ago
Rayukan

Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa daga karamar Salla zuwa yau an samu asarar rayuka akalla mutum 86 a babban titin Nnamdi Azikiwe da ke garin Kaduna, wanda aikin gyaran hanyar ya ki ci ya ki cinyewa.

A sakamakon aikin hanyar da ke tafiyar hawainiyya, akasarin wadanda suka rasa rayukansu, manyan motoci ne ke zama ajalinsu, kamar yadda wasu ganau, Dakta Muhammad Jamilu da Injiniya Muhammad Buhari, suka tabbatar mana da hakan.

Malam Muktar mai littafai Dan Mani, yana gudanar da ayyukansa kan babban titin, ya tabbatar da cewa irin abubuwa da ke faruwa a wannan babbar hanyar abin takaici ne, domin akwai ‘yan’uwansa da manyan motocin suka zama ajalinsu har lahira.

ADVERTISEMENT

Haka zalika, shi ma wani Bawan Allah mai suna Alhaji Nasiru Wagini, wanda shi ma ya bayyana cewa, akwai danuwansa mai suna Dakta Hamza Wagini wanda kemist dinsa ke kasuwar barci Kaduna, shi ma daga zuwa isar da wani muhimmin sako wata babbar mota ta buga kansa da kankaren titin wanda ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

A cewarsa, Alhaji Ado Baban Nazifi, mazaunin Unguwar Mu’azu Kaduna, shi ma daga zuwa kai kudin sadaki a Asukulaye kusa da masalacin Sheikh Dahiru Bauci, mota ta kashe shi har lahira.

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

Ya ce akwai wata mata da goyonta motar tirela ta takesu suka mutu a nan take, haka nan ma a ranar Lahadin da ta gabata, wata motar tirela ta sake halaka wani Bawan Allah mai suna Anas Abdulmumin Kura wanda aka fi sani da Albani, shi da dansa a daidai Kurmin Mashi kusa da sabuwar fanteka. 

Sai dai a kasantuwar rasa rayukan da ake yi a titin ya ta azzara sosai, hakan ya sa wasu mutane sun fara daukar doka a hannunsu, ta yadda wasu matasa ke kona mota da zaran hakan ya faru.

Jama’a da dama sun koka, inda suke kira ga mai girma Gwamna Jihar Kaduna, Malam Uba Sani da ya dube su da idon rahama ya dauki mataki, ya kuma ja hankalin gwamnatin tarayya da ta dauki mataki kawo karshen aikin wannan babbar hanyar, domin dakile cin rayukan al’umma da take yi.

Rayukan
Alkazeem M. Shariff
+ postsBio
    This author does not have any more posts.

MASU ALAKA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Manyan Labarai

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Labarai

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Next Post
Matsalar Tsaro: Gwamnati Ta Amince Da A Dawo Da Tsofaffin Sojoji Fagen Daga

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.