A yau Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce cikin watannin farko na rabin shekarar nan ta 2026, cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka ta bunkasa yadda ya kamata.
Kazalika, matakin Sin na kawar da daukacin haraji kan hajojin kasashen Afirka masu huldar diflomasiyya da ita ya haifar da ‘da mai ido. Lin Jian, ya ce a nan gaba kuma, Sin za ta kara zurfafa matakan kyautata cinikayya tsakaninta da kasashen na Afirka, tare da aiwatar da kwararan matakai na bude kasuwannin Sin ga hajoji masu inganci na nahiyar Afirka, da shigar da sabon kuzari, wajen gina al’umma mai makomar bai daya ta Sin da Afirka a dukkanin fannoni domin sabon zamani.
Lin, ya kara da cewa cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka cikin rabin farkon shekarar nan, ta gudana bisa wasu ma’aunai, wadanda suka hada da na farko, saurin bunkasar jimillar cinikayyar, inda ya zuwa yanzu, darajar hada-hadar cinikayya tsakanin sassan biyu ta kai yuan tiriliyan 1.41, adadi mafi yawa da aka taba samun a rabin farko na wata shekara.
Kazalika, ana sa ran jimillar cinikayyar tasu za ta kai sabon matsayi zuwa karshen shekarar nan ta bana.
Na biyu kuma, an samu kyautatuwar tsarin cinikayyar, inda wasu alkaluma suka nuna yadda kayan sarrafawa, da nau’oin da wasu masana’antun ke bukata daga wasu, suka kwashe kaso 75 bisa dari na jimillar hajojin Sin da ake fitarwa zuwa kasashen Afirka, wato irin hajojin da ake bukata wajen bunkasa masana’antun Afirka, da na zamanantar da ayyukan gona, sabanin wadanda ake saya domin amfanin jama’a kai tsaye.
Na uku kuma, ana kara fadada damarmakin shigo da hajojin Afirka cikin kasuwannin Sin. A watannin Mayu da Yunin bana, sakamakon fara aiwatar da manufar kawar da harajin fito kan kayayyakin kasashen Afirka da ake shigarwa Sin, darajar hajojin kasashen nahiyar da aka shigar kasar Sin, ta kai kudin Sin yuan biliyan 193.8, adadin da ya karu da kaso 23.5 bisa dari a mizanin shekara-shekara. (Saminu Alhassan)













