ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sakamakon Dangantakar Sin Da Afrika Na Taba Mutane Masu Rauni Da Karamin Karfi

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 month ago
Afrika

Tawaga ta 27 ta jami’an lafiya ta Sin a Saliyo, ta kaddamar da shirin horar da ma’aikatan jinya ko nas-nas dabarun likitancin gargajiya na Sin, wanda ya hada lakcoci daga masanan Sin ta hanyar na’urori da kuma wadanda jami’an lafiya na Sin da ke kasar za su gabatar kai tsaye, domin karfafa tsarin kiwon lafiya a kasar. Hakika faduwa ta zo dai-dai da zama. Watau yayin da nahiyar Afrika ke fama da yawan al’umma da karancin ci gaba da fasahohi da ma talauci da sauransu, inganta tsarin kiwon lafiya a nahiyar wani babban batu ne da zai taimaka wajen inganta yanayin rayuwar al’umma.

Yawancin lokuta, fargabar tiyata da rashin kudi su ne manyan abubuwan da ke hana mutane zuwa asibiti, amma da likitancin gargajiya irin na Sin da ke mayar da hankali kan gano tushen cuta da maganinta ba tare da tiyata ba, jama’a za su samu kwarin gwiwar zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu. Baya ga haka, horar da jami’an lafiya na nufin za su samu wata dabara ta daban, baya ga irin na likitancin yammacin duniya.

Haka zalika, yana nufin za su iya bayar da kulawa ko da babu jami’ai Sinawa. Wannan ma za mu iya bayyana shi da wani misali na yadda Sin ke gabatar da fasahohi da dabarunta ga sauran kasashe maimakon ta yi babakere ko ta kafa shinge.

ADVERTISEMENT

Bugu da kari, babban misali ne na burin Sin na samar da duniya mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama. Lallai hadin gwiwar Sin da nahiyar Afrika ya cancanci yabo, domin ya zarce batu na tattalin arziki da cinikayya, ya tsallake zancen ababen more rayuwa da musaya, kai tsaye yana taba mutane masu rauni da karamin karfi tare da haifar da sakamako na a zo a gani.

A shekarar 2023 aka cika shekaru 60 da Sin ta fara tura tawagogin jami’an lafiya zuwa ketare, kuma cikin wadannan shekaru 60 da suka gabata, Sin ta tura likitocinta fiye da dubu 30 zuwa kasashe ko yankuna 76, kana yawan mutanen da suka samu jinya kyauta ya kai miliyan 290.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Yanzu haka, akwai tawagogin lafiya na kasar Sin a wurare 115 a kasashe 56 dake fadin duniya, galibinsu wurare ne masu nisa da wahalar rayuwa. Kuma ba duba marasa lafiya kadai suke yi ba, suna aiwatar da tiyata da bayar da horo tare da musayar fasahohi tsakaninsu da dalibai da takwarorinsu likitoci, inda suke barin wani tambari da ba za a iya gogewa ba, domin mutanen da likitocin Sin suka yi jinyarsu, suna ci gaba da tunawa da su tare da yi musu fatan alheri. Wannan ita ce asalin dangantakar abota da ke taba al’umma, da kuma al’umma ke alfahari da ita. (Fa’iza Mustapha)

Afrika
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy
Afrika
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Sin Za Ta Ci Gaba Da Ingiza Kyakkyawan Yanayin Cinikayya Tsakaninta Da Nahiyar Afirka

Sin Za Ta Ci Gaba Da Ingiza Kyakkyawan Yanayin Cinikayya Tsakaninta Da Nahiyar Afirka

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.